Sabuwar Mota: Hazikin Dan Najeriya Ya Kera Motar G-Wagon Ya Kuma Tuka Ta a Cikin Gari, Bidiyon Ya Yadu
- An gano wani hazikin dan Najeriya yana tuka motar G-Wagon wanda ya kera da hannunsa a cikin gari
- A wani bidiyon TikTok da Kingsley Reigns Idoko ya wallafa, an gano yaron yana tuka motar a harabar cikin gida yayin da ahlinsa ke jinjina masa
- Masu amfani da TikTok na ta jinjinawa matashin yaron sannan wasu na kira ga a bashi tallafi
Jama'a a soshiyal midiya sun jinjinawa wani matashin yaro da ya kera motar G-Wagon bayan cin karo da wani bidiyo a TikTok.
Wani mai amfani da TikTok, Kingsley Reigns Idoko, shine ya wallafa bidiyon a ranar Asabar, 31 ga watan Disamba kuma ya nuno yaron yana tuka motar a cikin gari.
Matashin yaron ya tuka motar G-Wagon din a harabar gidansu kuma danginsa suna ta jinjina masa a kan wannan fasaharsa.
Dan Najeriya da ya kera motar G-Wagon
Motar da aka yiwa bakin fenti kuma ya yi kama da G-Wagon tana ta juyawa ba tare da wata matsala ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kingsley ya ce matashin kaninsa ne amma ya gaza bayanin yadda aka yi ya kera motar.
Ya rubuta a jikin bidiyon:
"Kanina ya kera wata motar G-Wagon dan Allah ku tayani yada shi."
Masu amfani da TikTok sun yabama yaron a kan wannan kokari nasa. Da dama sun yi kira ga a tallafawa mutane da suka nuna iyawarsu irin haka a bangaren fasaha.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@user7007593736174Episode ya ce:
"Mugun ido ba zai taba ganinka Amin...Allah ya kara daukaka dan uwa."
@gilberttimothy301 ya yi martani:
"Ma shaa Allah! Allah ya kara daukaka dan uwa."
@Anthony moris ya yi martani:
"Kana da makoma mai kyau."
@Sammy ya ce:
"Abu ya yi kyau! Amma dan Allah jire logon Toyotan nan sannan ka saka naka logon."
@user37531645809204 ya yi martani:
"Ina son sanin gayen nan."
@Maskman ya ce:
"Ya nemi nashi logon mai kyau da kansa, amfani da logon Benz kamar sadaukar da nasarar shi gare su ne."
Dalibin Jami'a Ya Kirkiri Motar Daukar Kaya a Matsayin 'Project' Dinsa
A wani labarin, wani dalibin jami'ar Benin ya kera wata motar daukar kaya a matsayin 'project' dinsa na jami'a.
Asali: Legit.ng