Zakulo Gaskiya: Shin Da Gaske Kwankwaso Ne Ya Fadi A Wurin Taron Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

Zakulo Gaskiya: Shin Da Gaske Kwankwaso Ne Ya Fadi A Wurin Taron Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

Wasu shafuka a dandalin sada zumunta sun yi ikirarin cewa Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP, ya fadi kasa a wurin kamfen dinsa.

A wani bidiyo da ya ke yawo da wani mai amfani da Facebook ya wallafa, ana iya ganin wani mutum da ake ce wai Kwankwaso ne tare da yan jam'iyya.

Bidiyon fadi kasa
Zakulo Gaskiya: Shin Da Gaske Kwankwaso Ne Ya Fadi A Wurin Taron Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa. Hoto: @thecable
Asali: Twitter

Mai amfani da Facebook din ya yi rubutu tare da bidiyon kamar haka:

"Daga karshe ya ga sakamakon rashawa. Na yi imanin an ware kudi mai yawa don gina mimbarin amma wanda aka bawa aikin ya yi aiki mara kyau ya soke sauran kudin a aljihunsa. Ga sakamakon hakan. #VoteWisely"

Kawo yanzu, kimanin mutane 1.2k ne suka kalli bidiyon.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Ta tabo inda yake so: Amarya ta shafa kirjin ango a wurin biki, ya cika mata jaka da daloli

A bidiyon da ke yawo, an hangi mutumin da aka ce wai Kwankwaso ne ya wani katako inda ya yi yunkurin gyarawa, jim kadan, shi da sauran yan jam'iyya suka fadi bayan katakon da ke mimbarin ya rushe.

Nan take wasu yan jam'iyya mafi yawancinsu sanye da jan hula, mabiyan Kwankwaso, suka taya shi ya tashi.

A Twitter, shafuka da dama sun wallafa bidiyon da rubutu daban-daban da ke nuni da cewa Kwankwaso ya fadi daga mimbari.

Kazalika, kafafen watsa labarai kamar Pulse, WithinNigeria, da 247ureports, da wasu sun wallafa rahoton, suna ikirarin Kwankwaso ne ya fadi wurin rali.

Amma Kwankwaso ne mutumin da ke bidiyon?

Binciken tantancewa

TheCable ta saka bidiyon a InVID, manhajar tantance bidiyo, nazarin da aka yi na hoton bidiyon ya nuna mutumin da ya fadi ba shi da kamanceceniya da Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Ta Shiga Aikin Soja, Hotunan Sauyawarta Sun Yadu

Binciken da The Cable ta yi ya nuna cewa mutumin da ake cewa Kwankwaso ne, sunansa Maliki Kuliya, tsohon kwamishinan shari'a na Kano.

An kuma tuntubi Abdullahi Rogo, kakakin NNPP don tabbatarwa idan dan takarar shugaban kasar jam'iyyar ne a bidiyon da ya bazu.

Rogo ya ce:

"A'a, karya ne. Ba Kwankwaso bane."

Yanke hukunci

Ikirarin cewa Kwankwaso ya fadi a wurin kamfen din shugaban kasa na NNPP ba gaskiya bane. Mutumin da ke bidiyon da ya bazu Maliki Kuliya ne ba Kwankwaso ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164