Aboki Ya Bindige Abokinsa 'Dan Sanda da Bindigarsa, Ya Tsere da Ita
- Wani mutum ya halaka abokinsa 'dan sanda mai mukamin kofur inda yayi amfani da bindigar 'dan sanda wurin halaka shi
- An gano cewa, mamacin mai suna Bob ya bar bindigarsa a kan benci inda ya tashi wanke cokali yayin da abokinsa David ya dauka yayi masa ruwan harsasai
- Lamarin ya faru a gaban wani bankin 'yan kasuwa wanda bayan nan David ya arce da bindigar 'dan sandan inda har yanzu ba a kama shi ba
Yenagoa, Bayelsa - Wani abokin 'dan sanda mai mukamin kofur ya harbe shi har lahira a farfajiyar wani bankin 'yan kasuwa dake jihar Bayelsa inda 'dan sandan ke gadi.
Wata majiya a bankin ta sanar da Daily Trust cewa, lamarin ya faru ne a ranar Laraba da ta gabata a farfajiyar bankin kan titin DSP Alameisegha dake Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa inda dukkansu ke cin abincin karan.
Majiyar tace yayin da 'dan sanda ya tashi ya bar bindigarsa a kan benci tare da zuwa wanke cokali, abokinsa ya dauka bindigar tare da harbinsa babu kakkautawa ta baya sannan ya tsere da bindigar.
Ya kara da sanar da Daily Trust cewa, mamacin ya gabatar da wanda ya kashe shi mai suna David ga jami'an bankin a makon da ya gabata matsayin 'dan uwansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda majiyar tace, bincike ya nuna cewa marigayin 'dan sanda 'dan asalin yankin Nembe ne yayin da wanda ake zargin da kashe shi 'dan Liama ne daga karamar hukumar Brass ta jihar.
An tattaro cewa, wanda ake zargi da kisan kan yana zama ne a farfajiyar bankin.
"Lamarin ya faru wurin karfe 12 na ranar Laraba yayin da dukkansu ke cin abincin rana. Yayin da mamacin 'dan sanda ya bar bindigarsa a kan benci inda ya tafi wanke cokali, makashin ya dauka bindigar tare da harbinsa babu kakkautawa ta baya.
"An hanzarta kai shi Cibiyar Lafiya ta Tarayya inda aka tabbatar da mutuwarsa washegari."
- Majiyar tace.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Beyelsa, SP Asinim Bustswat, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin yace an san wanda ya aikata mugun abun kuma ana cigaba da bincike don kama shi.
Yace:
"A ranar 29 ga watan Disamban 2022, wani 'dan sanda Kofur Bob dake aiki a wani banki dake Yenagoa abokinsa ya kashe shi yayin da yake tattaunawa a farfajiyar bankin. An san wanda ya aikata lamari kuma ana bincike don kama shi."
IGP ya magantu kan jami'in da ya harbe lauya a Legas
A wani labari na daban, sifeta janar na 'yan sandan Najerya, IGP Usman Baba Alkali, yayi Allah wadai da kisan lauya Bolanle Raheem.
Ya umarci hukumar 'yan sanda da ta gaggauta bincike a kai tare da gurfanar da wanda ake zargin.
Asali: Legit.ng