PSC ta Dakatar da ‘Dan Sandan da Ake Zargi da Bindige Lauya a Legas

PSC ta Dakatar da ‘Dan Sandan da Ake Zargi da Bindige Lauya a Legas

  • Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta dakatar da ASP Drambi Vandi, jami'in da ake zargi da bindige wata lauya mai juna biyu a Legas
  • Hukumar tace ta natsu tare da nazarin shaidun da aka mika gabanta inda tace ya dakata da aiki a take kuma a cigaba da bincike kan lamari
  • Ta kara da sanar da cewa za a mayar da hankali sosai wurin horar da 'yan sanda yadda ya dace kan sarrafa makamai

Legas - Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda, PSC, ta amince da dakatar da Drambi Vandi, ‘Dan sanda mai mukamin ASP wanda aka kama kan kisan wata Bolanle Raheem, kamar yadda jaridar TheCable ta rahoto.

Wannan amincewar an sanar da ita ne a wata takarda da aka fitar ta hannun Ikechukwu Ani, kakakin Hukumar Kula da Ayyukan ‘yan sanda ya fitar.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Sojoji sun ceto wata jami'arsu da aka sace, ake ta azabtarwa a daji

Bolanle Raheem
PSC ta Dakatar da ‘Dan Sandan da Ake Zargi da Bindige Lauya a Legas. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Dakatarwan na zuwa ne bayan sa’o’i kadan bayan da Usman Alkali, Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya ya bukaci hakan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jaridar TheCable ta rahoto cewa, Raheem, wacce ke dauke da juna biyu yayin mutuwarta, an harbe ta ne a ranar 25 ga watan Disamban 2022 a yankin Ajah dake jihar Legas.

Kamar yadda Ani, kakakin PSC ya bayyana, dakatarwan za ta fara aiki ne nan take.

“Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta amince da dakatar da ASP Drambi Vandi mai lambar aiki AP/no 134901 wanda ake zargi da harbi tare da kashe lauya Bolanle Raheem a ranar Kirsimeti a yankin Ajah dake jihar Legas. Dakatarwar zata fara aiki a take."

- Takardar tace.

“Hukumar a wata wasika da ta aike ga Sifeta Janar na 'yan sanda wacce mukaddashin shugaba Jastis Clara Bata Ogunbiyi ta saka hannu, tace hukumar ta lura cikin natsuwa kan shaidun da aka kawo mata kuma ta shawara tare da amincewa da dakatar da jami'in.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan APC Ya Garzaya Abuja Ya Gana da Sufetan Yan Sanda Na Kasa

"Wasikar mai taken 'Bukatar dakatar da AP/ NO 134901 ASP DRAMBI Vandi daga aiki' tana dauke da kwanan wata 28 ga Disamban 2022.
“Hukumar tun farko ta kushe kisan lauyar tare da bukatar bincike mai zurfi kan lamarin. Tayi kira kan horarwa mai kyau ga 'yan sanda kan amfani da makamai."

- Takardar ta shaida.

IGP ya magantu kan kisan lauyan Legas

A wani labari na daban, sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, IGP Alkali Usman Baba, ya kushe kisan Bolanle Raheem, lauyar Legas mai juna biyu da jami'in 'dan sanda ya bindige.

Ya bukaci a gaggauta bincike kan lamarin tare da gurfanar da wanda ake zargi inda da bukatar hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng