Kaduna: ’Yan Sanda Sun Kashe ’Yan Bindiga 21, Sun Ceto Mutane 206 da Aka Yi Garkuwa da Su a 2022

Kaduna: ’Yan Sanda Sun Kashe ’Yan Bindiga 21, Sun Ceto Mutane 206 da Aka Yi Garkuwa da Su a 2022

  • 'Yan bindiga akalla 21 aka kashe a jihar Kaduna cikin shekarar nan, kamar yadda kwamishinan 'yan sanda ya fada
  • An ceto mutane sama da 206 a 2022 bayan yin bata-kashi da 'yan bindiga a yankunan jihar ta Kaduna
  • An bayyana adadin 'yan ta'addan da aka kama da kuma yawan makaman da aka kwato cikin watanni kasa da 12

Jihar Kaduna - Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta bayyana ayyukan da ta yi na kame 'yan ta'adda da gurfanar dasu da ma sheke wasu a cikin 2022, Tribune Online ta ruwaito.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Yekini Ayoku ya bayyana cewa, rundunarsa ta kashe ‘yan bindiga 21 tare da ceto mutum 206 da aka sace a shekarar nan.

Kwamishinan ya kuma shaida cewa, akalla dabbobi 1,446 ne da ‘yan ta’adda suka sace a bangarorin jihar jami’ansa suka yi nasarar cetowa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Halaka Jigon Jam'iyyar PDP A Gidan Mahaifinsa

Aikin da 'yan sanda suka yi na magance matsalar 'yan bindiga a Kaduna a 2022
Kaduna: ’Yan Sanda Sun Kashe ’Yan Bindiga 21, Sun Ceto Mutane 206 da Aka Yi Garkuwa da Su a 2022 | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Hakazalika, ya zuwa karshen shekarar nan, an yi nasarar kwato bindigogi 49 daga hannun tsagerun ‘yan bindiga.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

'Yan bindiga 780 sun shuga hannun 'yan sanda

Ya kara da cewa, akalla wadanda ake zargi 780 ne suka shiga hannun jami’ai bisa zargin aikata laifuka daban-daban a jihar.

A cewarsa, an gurfanar da akalla 116 daga cikin wadanda ake zargin a gaban kuliya, kamar yadda rahoton Daily Trust ya tattaro.

A kalamansa:

“An kwato alburusai 1,359 da kuma babura 17 da ‘yan bindiga ke amfani dasu. Har ila yau, an kama buhunna 15 na wani busasshen ganye da ake zargin tabar wiwi ne.

Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da yawaitar hare-haren 'yan bindiga, duk da cewa a wannan shekarar an ce an samu sauki.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: IGP ya fadi abin da ya kamata a yiwa dan sandan da ya kashe wata lauya mai ciki

Sauran jihohin Arewa naso Yamma da ke fama da wannan matsala sun hada da Katsina, Zamfara, Neja da sauransu.

Za a haramtawa 'yan sandan Najeriya shan giya gaba daya

A wani labarin kuma, majalisar wakilai na duba kawo dokar da za ta haramta shan giya jami’an ‘yan sanda a Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan yiwa wata matar aure lauya mai juna biyu kisan gilla da dan sanda ya yi a jihar Legas.

Ana yawan samun tashin-tashina game da ayyukan ‘yan sanda, ana samun lokutan da suke sheke mutane babu dalili.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.