Kila CBN Ya Canza Shawara, Sanatoci Sun Ce a Ajiye Batun Canjin Kudi Sai Yunin 2023

Kila CBN Ya Canza Shawara, Sanatoci Sun Ce a Ajiye Batun Canjin Kudi Sai Yunin 2023

  • Majalisar dattawan kasar nan ta bada shawara ga CBN ya kara tsawon lokacin canza manyan kudi
  • Sanatoci su na ganin zai fi kyau a bari sai karshen Yunin 2023 sannan za a daina karbar tsofaffin kudi
  • A lokacin da aka yi zaman jiya, ‘Yan majalisa sun yi muhawara a kan canjin da ake kokarin kawowa

Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta roki babban banki na CBN ya tsawaita wa’adin da ya bada na canza tsofaffin kudi zuwa tsakiyar shekarar badi.

Vanguard ta ce majalisar dattawan ta na so lokacin da za a daina karbar tsofaffin kudi ya koma 31 ga watan Yuni maimakon karshen Junairun 2023.

A zaman da aka yi na ranar Laraba, 28 ga watan Disamba 2022 a majalisar dattawan kasar, an bijiro da maganar canjin manyan kudin da CBN ya yi.

Kara karanta wannan

Abin nema: Majalisa ta amince da bukatar Buhari, zai sake runtumo bashi mai yawa

Sanata Ali Ndume mai wakiltar Kudancin jihar Borno ya roki a kara lokacin da aka bada domin gudun a jefa mutanen Najeriya cikin halin ha'ula'i.

Mutane sun fara wahala a banki - Ndume

An rahoto Ndume ya ce tuni mutane sun fara fama da bin dogayen layi a bankuna, su na neman hanyar da za a ba su sababbin Nairorin da aka buga.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

‘Dan majalisar ya ce da zarar an fara raba sababbin kudin da aka fitar, ‘yan kasuwa za su rika gujewa tsofaffin kudin da ake shirin daina aiki da su.

Majalisa
Sanata Ali Ndume a Majalisa Hoto: @NgrSenate
Asali: Facebook

Bugu da kari, Sanatan na APC ya ce samun sababbin kudin yana wahala domin CBN ya yanke adadin kudin da mutum ko kamfani zai karba a rana.

“Idan ba a janye wa’adin daina amfani da kudi daga 31 ga watan Junairu ba, ‘Yan Najeriya da-dama za su samu kansu cikin wahalar rayuwa.

Kara karanta wannan

Ba Lallai Rashin Tsaro Ya Kare Ba a Najeriya Nan Da Shekaru 30, Inji Fitaccen Manazarci a Jami'ar BUK

A gujewa irin abin da ya faru a 1984 da aka canza kudi.”

- Sanata Ali Ndume

Aliero ya ce Ndume ya yi gaskiya

Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya, Muhammad Adamu Aliero ya ce a wasu kauyukan, mutane ba su da labarin an canza manyan kudin Najeriya.

Da ya mike domin ya yi jawabi, rahoton ya ce Sanata Muhammad Adamu Aliero ya goyi bayan Ndume, ta jara da cewa a kauyuka babu bankuna ko POS.

Legit.ng Hausa ta fahimci karin wa'adin shi ne ra'ayin Sanata Aliyu M. Wammako.

'Yan kasuwa za a bari da aiki

Hakan na zuwa ne bayan an canza takardun N200, N500, N1000, an maye gurabensu da wasu sababbin kudin da bankin CBN ya fitar kwanakin baya.

An samu rahoto Bankin Duniya ya tabbatar da cewa canjin takardun kudi da babban bankin CBN ya yi, zai fi tasiri ne kan ‘yan kasuwa da marasa karfi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari na Kokarin Dawo da Harajin da Isa Pantami Ya Hana a Kakaba a 2022

Gwamnan Babban bankin Najeriya ya na ganin canjin Nairorin zai rage buga kudin jabu, matsalar garkuwa da mutane, da boye kudi da wasu suke yi 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng