Majalissar Wakilai Na Neman Kawo Dokar Haramta Shan Barasa Ga ’Yan Sandan Najeriya

Majalissar Wakilai Na Neman Kawo Dokar Haramta Shan Barasa Ga ’Yan Sandan Najeriya

  • Majalisar wakilai ta bayyana bukatar a fara bincike kan jami'an 'yan sandan da ke kashe mutane babu wani dalili
  • Hakazalika, sun bukaci a kawo dokar da za ta haramtawa jami'ai shan giya da sauran kayan maye a fadin kasar nan
  • Ana yawan samun lokutan da 'yan sanda ke kwankwadar barasa a bakin aiki, ko kuma suke kashe mutane babu dalili

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta kasa na shirin kawo sabuwar dokar haramta shan barasa ga jami'an 'yan sandan Najeriya da ma sauran dukkan abubuwan maye masu kau da hankali.

Da suke amincewa da kudurin, 'yan majalisa sun amince cewa, ya kamata a yi gyara ga dokar 'yan sandan Najeriya.

Hakazalika, sun yi Allah wadai da yadda wani jami'in dan sanda ya hallaka wata lauya a jihar Legas a ranar kirsimeti, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Halaka Jigon Jam'iyyar PDP A Gidan Mahaifinsa

Majalisar wakilai na duba yiwuwar hana 'yan sanda shan giya
Majalissar Wakilai Na Neman Kawo Dokar Haramta Shan Barasa Ga ’Yan Sandan Najeriya | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Wannan batu na gyara dokar dabi'ar 'yan sanda ta samo asali daga batun gaggawa da dan majalisa Babajide Obanikoro na APC a jihar Legas ya kawo a gaban majalisar a ranar Laraba a Abuja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Suna kashe mutanen da ya kamata su kare rayukansu

Da yake bayani, Obanikoro ya koka da yadda ba tare da wani dalili ba, dan sanda zai harbe lauya wacce ke da juna biyu na watanni bakwai nan take.

Ya kuma tuna cewa, lamari irin wannan ya faru a ranar 7 ga watan Disamba, inda wasu jami'ai daga dai wannan ofishin 'yan sandan suka hallaka wani matashi bayan kame shi.

Ya bayyana damuwar cewa, hakan na yawan faruwa a fadin Najeriya, kuma 'yan sanda na yawan kashe mutanen da suka yi alkawarin za su kare, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: IGP ya fadi abin da ya kamata a yiwa dan sandan da ya kashe wata lauya mai ciki

A bangare guda, 'yan majalisar sun bukaci a yi cikakken bincike kan kashe wannan baiwar Allah da ma sauran wadanda 'yan sanda suka kashe ba gaira babu dalili.

Bidiyon 'yan sanda na shan barasa a fili

A wani bidiyon da aka yada, an ga lokacin da wasu jami'an 'yan sanda ke kwankwadar barasa ba kakkautawa a fili.

Jama'ar kafar sada zumunta sun bayyana martaninsu kan wannan lamari mai daukar hankalin gaske.

Ana ci gaba da fuskantar barasa daga halayen 'yan Najeriya, a makon da ya gabata aka harbe wata mata mai juna biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.