Zamfara: 'Dan Takarar APC Ya Gwangwaje Jama'ar da Luguden Jiragen NAF Ya Ritsa Dasu
- 'Dan takarar majalisar tarayya karkashin jam'iyyar APC na mazabar Bungudu/ Maru a Zamfara ya bada kyautar N50,000 ga kowanne cikin farar hula da lugude ya ritsa da su
- Hakan ya biyo bayan luguden wutar da NAF suka yi wa 'yan bindiga, sai dai cikin rashin sa'a ya ritsa da mazauna yankin Malele da Mutunji
- Kyautar ta riskesu ne yayin da yaje jajanta ma wadanda lamarin ya auku dasu a asibitin kwararru na Ahmad Sani Yariman Bakura
Zamfara - 'Dan takarar majalisar tarayya mazabar tarayyar Bungudu/Maru a Zamfara na jam'iyyar APC, Alhaji Abdulmalik Zubairu ya bada kyautar N50,000 ga kowanne daga cikin wadanda harbe-harben sojin saman Najeriya ya ritsa dasu.
Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya ta ruwaito yadda lamarin ya ritsa da mutane 19 daga yankunan Mutunji na garin Dansadau, dake karamar hukumar Maru, inda suke samun kulawar gaggawa a asibitin kwararru na Ahmad Sani Yariman Bakura a Gusau.
Zubairu ya bada kyautar ne yayin da yaje jajanta ma wadanda lamarin ya auku dasu a asibiti ranar Talata.
Kowannensu ya samu kyautar da 'dan takarar ya bada don rage radadi da tsananin rayuwar harin da aka dakile amma yazo da gardama.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya siffata lamarin a matsayin ba-zata kuma abun tausayawa.
"Na shiga cikin matsanantanciyar damuwa yayin da na samu labari mara dadi na mummunar lamarin.
"Kalma daya tak ba za ta iya bayyana irin damuwar da na shiga bisa aukuwar wannan mummunan lamarin mai ban takaici ba.
- A cewarsa.
"A matsayinmu na musulmai, ba mu da wani zabi da ya wuce mu amsa duk kaddarar da Allah ya jarabcemu da shi.
"Ina amfani da wannan damar ne don mika ta'aziyyata ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, sannan fatan samun waraka cikin gaggawa ga wadanda suke samun kulawa a asibiti da garin Dansadau."
Yanzu-Yanzu: Alkali Baba Ya Fusata da Kisan Lauyar Legas, Yayi Umarnin Bincike da Gurfanar da ‘Dan Sandan
- Kamar yadda ya kara da cewa.
"Buri na shi ne yadda zan samarwa matasa aikin yi tare da magance matsalar rashin tsaro idan naci zaben 2023."
- A cewarsa.
'Yan bindiga sun kai hari Zamfara da Sokoto
A wani labari na daban, miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki wasu yankunan jihar Zamfara da Sokoto inda suka halaka a kalla mutane 15 tare da yin garkuwa da wasu sama da 100.
Asali: Legit.ng