IGP Ya Bada Shawarar Dakatar da Jami’in da Aka Kama Bisa Laifin Bindige Bolanle Raheem
- Sufeto jana'ar na rundunar 'yan sandan Najeriya ya bayyana abin da ya kamata a yiwa jami'in da ya kashe wata jami'a
- Wani jami'in dan sanda ya bindiga wata lauya a jihar Legas ranar kirsimeti, jama'a sun shiga jimamin rashi
- Ana yawan samun aikin ganganci daga jami'an 'yan sanda, musamman kashe wadanda basu ji ba basu gani ba
FCT, Abuja - Sufeto janar na rundunar 'yan sanda, Usman Alkali Baba ya ba da shawarin a dakatar da wani jami'in dan sanda, Drambi Vandi bisa bayan kama biyo bayan bindige wata mata lauya, Bolanle Raheem.
Bolanle, wacce lauya ce kuma matar aure ta gamu da ajalinta a hannun Drambi, lokacin da ta yi arba dashi a jihar Legas a ranar Lahadin da ta gabata, TheCable ta ruwaito.
Lauyar an ce tana ma dauke da juna biyun tagwaye a lokacin da wannan dan sanda ya dirka mata bindiga ya kashe ta.
Batun shawarin IGP na zuwa ne ranar Laraba 28 ga watan Disamba daga cikin wata sanarwa da Myiwa Adejobi; kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya ya fitar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar sanarwar, dakatar da jami'in ya yi daidai da matakin ladabtarwa da hukumar ke dauka kan jami'an da ke saba doka da kuma daukar doka a hannu.
Aikinmu ne kare 'yan Najeriya, ba kashe su ba, inji IGP
A bangare guda, IGP ya tabbatarwa 'yan Najeriya, aikin 'yan sanda shine tabbatar da doka da oda tare da kare dukiya da rayukan 'yan kasa.
Hakazalika, ya bayyana cewa, za a tabbatar da adalci kan Drambi bisa laifin da ya aikata daidai da tanadin dokar 'yan sanda.
Har ila yau, ya bukaci jama'a da su yi hakuri su kuma dauke kai daga daukar doka a hannunsu.
Ya kuma bayyana cewa, rundunar na aiki don tabbatar da mai yiwuwa don kare sake faruwar hakan a nan gaba.
Bidiyon yadda 'yan sandan Najeriya ke kwankwadar giya a bakin aiki, an yi martani
A wani bidiyo kuma, an ga lokacin da jami'an 'yan sanda ke kwankwadar barasa a cikin mutane, lamarin da ya girgiza intanet.
Rundunar 'yan sanda ta ce sam ba halin jami'anta bane shan kayan maye a bakin aiki, ta ce hakan ya saba da doka.
Jama'a suna ci gaba da kai karar jami'an 'yan sanda da ke nuna munanan dabi'u a cikin al'umma.
Asali: Legit.ng