An Kama Basarake a Zaria da Zargin Yin Lalata da Yaro Namiji Mai Shekara 14

An Kama Basarake a Zaria da Zargin Yin Lalata da Yaro Namiji Mai Shekara 14

  • An kama wani fitaccen basarake a jihar Kaduna bisa zargin lalata da karamin yaro bayan yaudararsa da aike
  • Rundunar 'yan sanda ta ce tana ci gaba da bincike don gano tushen lamarin kafin daga bisa a gurfanar da basaraken
  • Majiya daga asibitin da aka yiwa yaron gwaje-gwaje sun tabbatar yadda lamarin ya faru da kuma yadda jami'an 'yan sanda suka shiga batun

Zaria, jihar Kaduna - An kama Shehu Umar, Chiroman Barayan Zazzau a jihar Kaduna bisa zargin tursasa wani karamin yaro tare da yin lalata dashi, kamar yadda ya fito a rahotanni.

Wannan na fitowa ne daga bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammaed Jalige a lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Zaria, Aminya ta ruwaito.

A cewar kakakin na ‘yan sanda, ana ci gaba da bincike don gano tushen lamarin yayin da ake ci gaba da tsare basaraken a a hannun hukuma.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Da Aka Tura Gidan Kaso Ya Bayyana Darasin Da Koya a Zaman Da Ya Yi a Kurkuku

An kama basarake a Zaria da zargin yin lalata da karamin yaro.
An Kama Basarake a Zaria da Zargin Yin Lalata da Yaro Namiji Mai Shekara 14 | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Hakazalika, ya ce da zarar bayanai sun kammala kankama, za a gurfanar Shehu a gaban kotu domin nemawa yaron adalci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda lamarin ya faru

Mazauna unguwar da basaraken suke sun shaidawa majiya cewa, dama sun dade suna zarginsa da aikata irin wannan mummunan dabi’a kusan shekaru 20 da suka shude.

Yayin da jaridar Aminiya ta zanta da dan uwan yaron, ya bayyana cewa, lamarin ya faru a gidan basaraken da ke unguwar Kwarbai a cikin kwaryar Zaria.

Zubairu, wanda shine dan uwan yaron ya kuma shaida cewa, basaraken ya yi amfani sanayyar da ke tsakaninsa da yaron ne ta hanyar aikensa dakinsa don dauko masa kudi.

Bayan shigar yaron ne basaraken ya bi shi, ya rife kofa inda ya aikatar barnar da ya aikata bayan fitar da wuta tare da barazanar yanka shi idan ya yi ihu, haka nan Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kudi da lokaci za ka bata: Babban attajiri a Kudu ya shawarci Peter Obi ya janye daga takara

Bayan fitowarsu, yaron ya koma gida a dimauceinda ya garzaya ya shaidawa kanwar mahaifiyarsa da ita kuma ta sanar da iyayen abin da ya faru.

Matakin da ake dauka a hukumance

Bayan haka ne iyayen suka tara karfi da karfe a tsakanin ‘yan uwa tare alanta daukar matakin doka da ya dace, daga na suka kai kara ofishin ‘yan sandan yanki da ke Zaria.

A bangare guda, majiya ta ce ta garzaya cibiyar kula da cin zarafin yara a asibitin Gamba Sawaba, kuma an ce anan ne aka yiwa yaron gwaje-gwajen da suka dace.

Hajiya Aishatu Ahmed, shugabar sashen ta tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana cewa:

“Jami’an ’yan sanda da ke Fada, Zaria sun kawo yaron don a duba lafiyarsa, tare da wadda ake zargin ya aikata fyaden kuma mun bai wa ’yan sanda sakamakon bincikemmu.”

Ana yawan samun matsaloli irin wadannan na cin zarafin yara, kwanakin baya aka zargi rundunar sojin Najeriya da zubar da ciki ga mata sama da 10,000 da ke da alaka da Boko Haram.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Alkali Baba Ya Fusata da Kisan Lauyar Legas, Yayi Umarnin Bincike da Gurfanar da ‘Dan Sandan

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.