Labarin Mutumin da Ke Sana’ar Acaba da Jaririnsa a Cikin Riga Ya Jika Zukatan Jama’a

Labarin Mutumin da Ke Sana’ar Acaba da Jaririnsa a Cikin Riga Ya Jika Zukatan Jama’a

  • Joram Kimani, wani mutum da ke sana'ar acaba dauke da jariri a cikin rigarsa ya ba da labarin rayuwarsa
  • Mutumin ya bayyana cewa, matarsa ta gujeshi bayan da ta haifa masa jariri, kuma har yanzu dai bai san dalili ba
  • Tun bayan tafiyarta, ya gaza barin yaron a wani wuri ya tafi aiki, tun daga nan ya dauki kudurin ci gaba da tafiya da yaron a tare dashi

Wani mutum, Joram Kimani ya roki matarsa ta dawo gareshi, inda yace a shirye yake ya ci gaba da rayuwa da ita idan ta amince.

Kimani ya shaidawa Afrimax cewa, ya rasa matarsa ne bayan da ta haifa masa jariri, ta kama hanyarta ta yi tafiyarta.

Ya bayyana cewa, a baya yana aikin kwandastan mota bas a Kenya, kuma yana kiwon Aladu, wanda daga ribarsu ya samu kudin siyan babur din yin 'kabu-kabu'.

Kara karanta wannan

Ka latsa ni: Kyakkyawar budurwa ta tari wani dan Najeriya, ta nemi su fara soyayya

Yadda wani mutum ke sana'ar acaba da jariri a cikin rigarsa
Labarin Mutumin da Ke Sana’ar Acaba da Jaririnsa a Cikin Riga Ya Jika Zukatan Jama’a | Hoto: YouTube/Afrimax.
Asali: UGC

Ya kuma shaida cewa, matarsa ta fara nuna wani hali ne tun lokacin da ta dauki juna biyu jim kadan kafin ta haihu ta guje shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Abubuwa sun yi kamari kasancewar ina bukatar yin aiki don iya rike kaina sannan jaririn ya yi kankanta na barshi shi kadai."

Wannan lamarin ne yasa Kimani yace bai da zabin da ya wuce yake sanya yaron a cikin rigarsa don fita sana'ar acaba a madadin barinsa a gida.

Yaron har ya saba

Ya kuma gano cewa, rufin dakinsa ya fara yoyo, inda yace komai zai iya faruwa idan ruwan sama ya sauka.

Dalilin da yasa yake tafiya da yaron kuwa, saboda an san masu sana'ar acaba da sanya riguna masu nauyi, wanda a nasa bangaren ya zama sabbo ga wannan jariri.

Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Kama Hayan Ɗaki 1, Ta Shirya Shi Tamkar 'Aljannar Duniya' Da Sabon Firinji, Talabijin Da Kayan Ɗaki

"Nakan sanya jaririn a ciki sannan na bar kofa ta sama ta yadda zai iya numfashi."

Ya kuma shaida cewa, jaririn yanzu haka ya ma saba da wannan rayuwar, da kansa yake shiga cikin rigar idan lokaci ya kankama.

Ya ce, kafin ya bar gida, yakan daga fate ya sanyawa jaririn kunzugu, kuma yakan sauya kunzugun duk sadda jaririn ya totsa toroso.

Yanzu dai yana neman taimako daga al'ummar yanar gizo, domin yana cikin wani yanayi mara dadi na tsananin talauci.

Martanin jama'a a kafar sada zumunta

Phai Matsele:

"Kai misali ne ga dukkan maza masu 'ya'ya da suka ras amatansu, don Allah ya rike wannan lamari. Tuni dama an albarkace ka."

Marcia Dunkley:

"Allah yana kallon komai game da kai dan uwa. Allah zai ba ka fiye da abin da zaka iya, abubuwa za su juya gare ka da danka."

Salito Salina:

"Allah ya maka albarka, uba na gari a wannan rana. Babu bukatar ta dawo, bata tausayin wannan talikin jaririn."

Kara karanta wannan

Kamar da wasa: Amarua ta ce ba za a daga bikinta ba, ta zo wurin biki da ciwo a kafa

Maureen Randiki:

"Kai uba ne mai kulawa sosai, Kasancewar ka rike wannan yaron, Allah ya albarkace ka kuma ba za ka taba rasawa ba. Allah ya biya maka bukatunka."

A wani labarin kuma, amarya aka nema aka rasa yayin da kowa ya zo wurin daurin aure, an yi ankon N150k.

Asali: Legit.ng

Online view pixel