An Sanar da Wuri, Rana Da Lokacin Da Wike Da Gwamnonin Da Sukayiwa Atiku Tawaye Zasu Sanar Da Zabinsu
- Nan da yan kwanaki Gwamna Nyesom Wike da sauran gwamnonin da suka yiwa Atiku tawaye zasu yanke shawara
- An tattaro cewa Wike da sauran gwamnonin 4 zasu bayyana dan takaran shugaban kasan da zasu yi ranar Alhamis, 5 ga Junairu
- Wata majiya ta bayyana cewa zasu sanar da wannan ne lokacin kaddamar da kamfen Gwamnan Oyo za'a yi wannan sanarwa
Gwamnoni 5 na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da suka yiwa dan takarar shugaban kasan jam'iyyarsu, Atiku Abubakar, tawaye zasu sanar da wanda zasu goyawa baya a zaben 2023.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wadannan gwamnoni karkashin gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers zasu sanar ne ranar Alhamis, 5 ga watan Junairu, 2023.
Gwamnonin sun hada da gwamnon Nyesom Wike (Rivers), Seyi Makinde (Oyo), Okezie Ikpeazu (Abia), Samuel Ortom (Benue), da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ana hasashen cewa zasu marawa dan takarar shugaban kasan Labour Party, Peter Obi, baya.
Idan hakan ya tabbata, wannan babban kalubale ne ga Alhaji Atiku Abubakar a zaben 2023.
Obasanjo Na Tare da Gwamnonin G-5
Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, tuni ya yi kira ga Gwamnonin G-5 su marawa Peter Obi baya.
A cewar majiyar:
"Gwamnonin na tunanin bin shawaran Obasanjo ne cewa dan kudu ne ya kamata ya zama shugaban kasa a 2023. Obasanjo ya basu shawaran su marawa Obi baya saboda yana ganin koda mulki zai koma kudu, yankin Kudu maso gabas suka yi cancanta."
"Wannan shine dalilin da ya sa a zamansu na karshe a Landan, ya ce zaben Obi shine adalci."
Majiyar ta kara da cewa lallai maganar Wike na cewa a Junairu zasu bayyana matsayarsu gaskiya ne, yace:
Yanzu Yanzu: Tinubu Ya Shiga Sabon Matsala Yayin da PDP Ta Saki Jerin Gwamnoni da Sanatocin APC Da Ke Yiwa Atiku Aiki
"Gwamnonin zasu sanar da dan takaran da zasu yi mako mai zuwa. Idan babu wani babban taro gabanin 5 ga Junairu lokacin da zai kaddamar da kamfensa, zasu sanar a ranar a Ibadan."
Adawa da Atiku: Shehu Sani ya ce gwamnonin G-5 na PDP su zabo koma waye su fada
Sanata Shehu Sani ya yi kira ga gwamnonin G-5 na PDP su fito su bayyana dan takarar da suke so koma wanene shi.
Ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar a shafinsa na Tuwita.
Asali: Legit.ng