'Yan Ta'adda Sun Halaka Mutum 15, Sun Jigata Wasu a Zamfara da Sokoto
- 'Yan bindiga dadi sun halaka a kalla mazauna 15 tare da barin mutane 8 cikin mawuyacin hali a wasu yankunan jihar Zamfara da Sakkwato
- Wani mazaunin yankin Ruwan Bore ya bayyana yadda ya tsallake rijya da baya yayin da hatsabiban suka auka wa yankin a babura sama da 100
- Har ila yau wani mazauni yankin ya ce yanzu 'yan bindigar basa wasan buya da jami'an tsaro, suna kai farmaki ne duk sanda suka ga dama
A kalla mutane 15 sun rasa rayukansu yayin da mutane da dama suka samu raunuka gami da samun kulawa a asibiti bayan 'yan bindiga sun auka yankuna a Zamfara da Sakkwato a yammacin Litinin, kamar yadda wani mazaunij yankin ya bayyana.
Anguwannin da aka hara sun hada da: Ruwan Bore a Zamfara da Gatawa, Dangari da Kurawa a jihar Sakkwato.
Batan Bindigu 2 na Lawalli Damina Ya Janyo Kisan Mutum 32 da Garkuwa da Dukkan Mazan Kauyen Randa a Zamfara
Wani mazaunin yankin wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyanawa BBC Hausa yadda 'yan ta'addan suka yi dirar mikiya kauyen a yammacin Litinin tare da budewa mazaunan wuta.
Na tsallake rijya da baya
"Sun zo a babura sama da 100. Mata da musamman yara, a yanzu sun bar yankun zuwa Kwatarkwashi don tsera kawunansu. Mu (maza) mun tsaya don yin jana'izar gawawwakin."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Wadannan mutanen ('yan ta'adda) sannannu ne. Su ba a wata duniyar suka zo ba. An san iyayensu da iyalansu, don me ake barinsu suna kashe salahan bayi?
"Ko wancan makon da ya gabata, sun sanya harajin 4 miliyan ga mazauna yankin Gora sannan sun tafi kauyen da motocin kwashe kaya, inda suka karba ta karfi da yaji buhuna 130 na hatsi."
- A cewar majiyar.
A Sakkwato, wani mazaunin yankin Nura Mamman ya labartawa Premium Times ta waya yadda maharan suka auka Dangari wurin karfe 2:00 da mintoci na rana.
"Ina cikin gidana yayin da naji kururuwan mata da yara. A lokacin, 'yan bindiga suna kokarin aukuwa yankin amma wata tawagar soji da 'yan sanda tare da 'yan sa kai suka yi kokarin korasu. Kasan yadda suka saba kai farmaki, sun raba kansu gida biyu ko ma fiye da haka, wannan karon sun zo da yawa.
"Jami'an tsaron basu iya dakilesu ba saboda yadda suke dauke da miyagun makamai."
- A cewar Mamman, wanda ya kammala digirinsa na farko a jami'ar jihar Sakkwato.
Daga Dangari, Premium Times ta tattaro yadda 'yan ta'addan suka auka yankin Gatawa da Kurawa duk a cikin karamar hukumar Sabon Rima na jihar.
Basharu Guyawa, wani mazaunin karamar hukumar Isa ya bayyanawa Premium Times yadda a karshen daren Litinin, aka kirga gawawwakin mutane 11 daga yankuna uku bayan mutane da dama da suka samu raunuka.
Guyawa, wanda shine shugaban Rundunar Adalci, wata kungiyar kare hakkin bil'adama a jihar Sakkwato, ya bayyana yadda harin 'yan bindigan bai zama bakon abu a gunsu ba.
"Hare-hare ba bakon abu bane kuma abun da ban tsoro saboda sama da shekaru daya yanzu, 'yan bindiga suna kai farmaki ne duk sanda suka ga dama. Yanzu sun daina jirin dare ko wasan buya da jami'an tsaro.
"Jiya sun zo da tsakar rana gami da budewa salihan bayi wuta. A yanzu da nake magana da kai, an tabbatar da mutuwar mutane 11 a wadannan yankunan tare da a kalla mutane takwas a mawuyacin hali kwance gadon asibiti."
- A cewarsa.
Sai dai, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sakkwato, Sanusi Abubakar, bai amsa kiraye-kirayen waya da sakonnin kar ta kwana da aka tura masa ta waya ba game da harin.
Asali: Legit.ng