Ba Lallai Ne Ta’addanci Ya Kau Ba Har Nan Da Shekaru 30 Masu Zuwa – Farfesa Ibrahim

Ba Lallai Ne Ta’addanci Ya Kau Ba Har Nan Da Shekaru 30 Masu Zuwa – Farfesa Ibrahim

  • Shahararren malami a jami’ar BUK, Farfesa Bello Ibrahim, ya koka kan lamarin tsaro a yankin arewacin Najeriya
  • Farfesa Ibrahim ya ce idan har ba a magance matsalolin talauci da rashin ilimi a arewa ba, ta’addanci ba zai kau ba har nan da shekaru 30
  • A cewar kwararren masanin halayyar dan adam da wadannan matsalolin ne miyagu ke samun cin galaba kan matasa cikin sauki

Kano - Wani shahararren malami a jami'ar Bayero na Kano, Farfesa Bello Ibrahim, ya yi gargadin cewa ta'addanci da fashi da makami da ya addabi yankin arewa na iya ci gaba har zuwa shekaru 20 zuwa 30 masu zuwa.

Malamin wanda ya kasance farfesa a bangaren sanin halayyar dan adam ya alakanta hasashensa ga manyan kalubale na talauci da rashin ilimi da ke addabar yankin arewacin kasar, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Daga Shiga Motar Haya a Titi, An Halaka Matasa 3 Tare da Cire Sassan Jikinsu

Sojoji
Ba Lallai Ne Ta’addanci Ya Kau Ba Har Nan Da Shekaru 30 Masu Zuwa – Farfesa Ibrahim Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

An tattaro cewa talauci da rashin ilimi sune manyan dalilai biyu da ke kara rura wutan rikicin da ake fama da shi a yankin.

Cikin sauki miyagu ke sauya tunanin matasa marasa ilimi da masu fama da talauci

Farfesa Ibrahim ya yi gargadin ne yayin da yake jawabi a bikin haduwar daliban Sashen Nazarin Halayyar dan Adama na Jami’ar BUK, ajin 2008.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Akwai binciken da aka gudanar inda aka gano cewa matasa tsakanin shekaru 18-25, musamman a jihohin Borno da Yobe basa zuwa makaranta. Don haka, idan gurbatattun mutane suka same su, suna iya juya su cikin sauki.
"An bar wadannan mutane sakaka babu ilimin addini da na boko. Sai dai idan an dauki mataki kan wadannan matsaloli (talauci da rashin ilimi), amma bana hango wucewar wadannan matsalolin."

Tun farko, shugaban tsoffin dalibam Sulaiman Aminu Abubakar, ya ce an shirya taron ne ba wai don haduwa a gaisa kawai ba bayan shekaru 14 da kammala makaranta.

Kara karanta wannan

Matsanancin Halin Talaucin da za ka bar mu Ciki ya fi Wanda ka Tarar da mu, Kukah ga Buhari

Ya ce an shirya taron ne don tara kudade domin taimakar iyalan mamatan cikinsu da kuma aiwatar da ayyukan da zai inganta ilimi a jihar, rahoton Aminiya.

Ya yi bayani cewa:

"Makasudin wannan taruwa shine don mu hadu, ba za mu iya cewa gwamnati kadai ce za ta kula da komai, mun ga cewa a matsayinmu na tsoffin dalibai da ke aiki a wurare daban-daban a yanzu muna da tamu gudunmawar da za mu iya bayarwa.
“Tsoffin dalibai na yin muhimman ayyuka a jami'a da garuruwansu, kuma akwai wurare da dama da za mu iya bayar da gudummawa a Kano. Muna fata a karshen wannan taron za mu tara abin da za mu aiwatar da akalla aiki daya a wata makarantar firamare ko sakandare ko ma jami'a a jihar."

Atiku ya yi alkawarin ba matasa aiki idan ya gaje Buhari

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya ce mata da matasa za su sha romon dadi idan ya yi nasarar darewa kujerar Buhari a zaben 2023.

Atiku ya ce zai mayar da hankali sosai wajen inganta rayuwar matasa da mata a gwamnatinsa ta hanyar basu aikin yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng