Bamu Gamsu a Rataye Malaminmu Ba, Daliban Abduljabbar Sun Ce Za Su Daukaka Kara
- Almajiran Abduljabbar sun tado da wani batu mai daukar hankali, inda suka ce ba za su amince a rataye malaminsu ba
- Sun zargi hannun gwamnan jihar Kano Ganduje a hukunta malamin nasu, sun ce dama suna zaman doya da manja
- An yankewa Abduljabbar hukuncin kisa ne ta hanyar rataya bayan kama shi dumu-dumu da laifin batanci ga ma’aiki SAW
Jihar Bauchi - Kwanaki bayan yanke masa hukuncn kisa ta hanyar rataya, daliban Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara sun fito sun bayyana matakin da za su dauka kan hukuncin kotu.
Kotu ta kama Abduljabbar da laifin cin zarafin ma’aiki SAW a cikin karatukansa, inda aka ce ya yi batanci da kuma furta kalamai masu kama da sukar addini.
Da suke martani ga hukuncin, sun ce za su daukaka kara saboda basu gamsu a rataye malaminsu ba kan laifin da basu yarda ya aikata ba, Aminiya ta ruwaito.
Almajiran nasa a karkashin tafiyar 'Ashabul Kahfi Warraqeem' reshen jihar Bauchi sun ce, akwai lauje cikin nadi, kuma lamarin siyasa ya shiga hukuncin da aka yankewa malamin nasu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akwai hannun Ganduje a lamarin nan, inji almajiran Sheikh Abduljabbar Kabara
A cewarsu, babu shakka hukuncin da aka yankewa Abduljabbar yana da nasaba da rashin jituwarsa da gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Hakazalika, sun ce dama a baya malamin nasu ya yiwa Ganduje kaca-kaca kan zarginsa da ake da kalmashe kudin talakawa da kuma almundahana, rahoton jaridar Leadership.
Abdullahi Musa, wani daga cikin almajiran ya bayyana halin da ake ciki a yanzu, ga kuma abinda yace:
“Ba mu gamsu da hukuncin ba domin muna zargin akwai hannun Gwamnan Jihar Kano da ma wasu malamai da suka dade suna zaman doya da manja da shi (Abduljabbar), wadanda suka yi kakaba masa laifin yin batanci ga ma'aiki don kawai su kawar da shi daga duniya ta hanyar amfani da karfin kotu.”
Bamu gamsu da hukuncin kotu ba, daliban Abduljabbar
A tun farko, jim kadan bayan yanke hukuncin ne daliban nasa suka shaidawa BBC Hausa cewa, akwai lam'a a hukuncin alkali, don haka basu gamsu ba.
Sun bayyana cewa, akwai kura-kurai da alamomin tambayoyi dangane da hukuncin da aka yankewa malamin nasu.
A tun farko, kotun ta ba Abdujabbar damar daukaka kara, kuma ana ci gaba da jiran martanin malamin ko dalibansa ko za su daukaka karar.
Asali: Legit.ng