Sojoji Sun Sheke ’Yan Boko Haram 8, Sun Kama 1 da Ransa, Sun Kwato Babura 4
- Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kashe wasu ‘yan ta’addan Boko Haram 8 a wani samame da suka kai
- Sun kuma yi nasarar kame wani kasurgumin dan ta’adda daga cikin ‘yan ta’addan a raye, sun kwato makamai da yawa
- Rundunar sojin na ci gaba da samun bayanan sirri tare da kakkabe maboyar ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabashin Najeriya
Mafa, jihar Borno - Rundunar sojin Operation Hadin Kai tare da hadin gwiwar ‘yan banga a daren ranar Litinin sun kasha ‘yan ta’addan Boko Haram takwas tare da kame wani da ransa a wani samamen da suka kai a karamar hukumar Mafa.
Wannan na fitowa ne daga bakin shugaban hafsun sojin Najeriya, Lt-Gen. Farouk Yahaya, inda ya nemi jami’ansa da suke ci gaba da ba ‘yan ta’adda kashi a dajin Sambisa da yankin tafkin Chadi.
An tattaro cewa, an yi nasarar kai wannan samame ne tare bayan samun wadatattun bayanan sirri daga Ngoum wani yanku da ke kusa da Maiduguri, kuma hakan ya kai ga hallaka ‘yan ta’addan.
Yadda aka gano maboyar 'yan bindiga
Wata majiyar sirri ta tsaro ta shaidawa Zagazola Makama, wani kwararre kan harkokin tsaro cewa, ‘yan ta’addan da aka kashen sune masu yawaita kai hare-haren fashi a yankunan kananan hukumomin Mafa, Jere da Konduga a jihar Borno.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majiyar ta shaida cewa:
“Jami’anmu sun kashe takwas daga cikinsu, sun kama daya a raye, sun kwato babura guda hudu da bindigogi kirar AK-47.”
A bangare guda, a wani aikin da wasu jami’an tsaron ya kai ga kashe wasu ‘yan ta’addan Boko Haram a wani aikin da suka gudanar.
Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da samun nasara kan ‘yan ta’adda a kasar nan, musamman a yankunan Arewa masu Gabashi.
An kai hari wani yankin Kaduna, sojoji sun dakile harin
A wani labarin kuma, bayan yin jana’izar mutane da yawa wadanda ‘yan ta’adda suka kashe, tsagerun sun sake kai mummunan hari a jihar Kaduna.
Wannan lamari ya faru ne a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna, daya daga yankunan da ke fama da yawaitar harin ‘yan bindiga.
Sai dai, a wannan karon basu kai ga nasara ba, domin an yi nasarar samun sojojin da suka fatattake su tare da kubutar da jama’ar da kadan ya hana a sace su.
Asali: Legit.ng