Garkuwa da Mutane: ‘Yan Bindiga Sun Karbi N60m, Sannan Sun Kashe Yara 3 ‘Yan Gida 1

Garkuwa da Mutane: ‘Yan Bindiga Sun Karbi N60m, Sannan Sun Kashe Yara 3 ‘Yan Gida 1

  • ‘Yan bindiga sun dauke ‘ya ‘yan wani mai saida shanu, sun bukaci sai an biya kudin fansa na N100m
  • A karshe sun rage kudin da suke so uwa N60m, kuma ‘yanuwan wadannan Bayin Allah suka biya kudin
  • Amma wannan bai kubutar da mutanen nan uku da aka dauke ba, duk da haka sai da aka hallaka su

Taraba - Ana zargin masu garkuwa da mutane da hallaka wasu mutane uku wanda ‘yan gida daya ne da kuma wani ‘dan acaba bayan sun karbi kudi.

Daily Trust ta ce ‘yan bindigan sun kashe wadannan mutane uku da mai acaban ne duk da an biya su har Naira miliyan 60 a matsayin kudin fansarsu.

Wannan lamari ya auku ne a kusa da dajin Garin Dogo da ke karamar hukumar Lau a jihar Taraba a ranar Lahadin nan da ta wuce, 25 ga Disamban 2022.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Kwana 1 da kashe tarin mutane, 'yan bindiga sun sake kai mummunan hari a Arewa

Rahoton ya nuna mutanen da aka dauke a dajin Garin Dogo duk ‘ya ‘yan mutum guda ne, ‘yan bindigan sun ce dole sai an biya N100m kafin su sake su.

N100m ya dawo N60m

Wani dillalin shanu, Alhaji Musa shi ne mahaifin yaran, shi ne ya rika tattaunawa da ‘yan bindigan domin ganin ya iya biyan kudin da suka bukata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da samun N100m ya gagra, sai ‘yan bindigan suka yarda cewa a biya N60m domin a saki ‘ya ‘yan na Alhaji Musa da ‘dan acaban da ya je biyan kudin.

'yan sanda
Wasu 'Yan sanda a bakin aiki Hoto:@PoliceNG
Asali: Twitter

Bayan ‘yan bindigan sun karbe kudin da aka kawo, sai suka kashe duka mutane hudun. Rahoton ya ce an birne wadannan Bayin Allah ne a kauyensu.

An yi irin haka a Sardauna

A karamar hukumar Sardauna duk a Taraba, wasu migayu biyar da ake zargin ‘yan bindiga ne sun mutu a hannun sojoji, abin ya faru ne a Maisamari.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Wani Kazamin Hari Jihar Arewa, Sun Kashe Basarake

Jami’an tsaro sun ce wadannan mutane da aka kama ne suka addabi karamar hukumar Sardauna da fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Taraba, DSP Usman Abdullahi ya tabbatar da aukuwar abin. An fitar da wannan labari a shafin Linda Ikeji a dazu.

Haka aka yi a Kogi

A wani rahoto daga Daily Trust, an ji yadda 'yan bindiga suka kashe wata mai suna Jummai Usman Daniel wanda aka yi garkuwa da ita a jihar Kogi.

Na kusa da Jummai Usman Daniel sun biya N300, 000 domin a fanshe ta, amma aka kashe ta. Abin ya faru ne a Ogane-aji a kauyen Anyigba da ke Dekina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng