Hukunci 11 da Alkalai Suka Yanke a 2022 da Za a Dade ba a Manta da su a Tarihi ba
- A shekarar nan ta 2022 mai shirin ficewa, an yi wasu hukunci a kotu wadanda za a dade ana labarinsu
- Daga ciki akwai wanda kotun tarayya ta tsige Gwamna David Umahi saboda ya sauya-sheka zuwa APC
- Akwai shari’ar Nnamdi Kanu da Gwamnatin tarayya da sabanin Hukumar INEC da jam’iyyun siyasaNnamdi Kanu
A wannan rahoto, The Cable ta tattaro shari’o’i masu zafi da aka yi a kotu a wannan shekarar.
1. INEC vs Jam’iyyun siyasa
An bude farkon shekarar nan da shari’ar Hukumar INEC mai shirya zabe a Najeriya da wasu jam’iyyun siyasa da aka sokewa rajistarsu saboda sun gaza cika sharudan kafuwa.
A dalilin soke masu rajista da aka yi, jam’iyyun suka taru suka shigar da kara a kotu, su na kalubalantar ikon INEC. A karshe kotun daukaka kara ta tabbatar da gaskiyar hukumar.
2. Tunbuke David Umahi
Mai shari’a Inyang Ekwo a babban kotun tarayya na Abuja ya sauke David Umahi and Eric Kelechi daga kujerar Gwamnatin jihar Ebonyi saboda sun bar PDP a karshen shekarar 2020.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Alkalin ya ce kuri’u 393,042 da Gwamnan ya samu a zaben 2019 na jam’iyyar PDP ne ba APC. Bayan watanni, kotun daukaka kara tayi watsi da hukuncin, ta bar Umahi a kujerarsa.
3. Amaechi da Gwamnatin Ribas
Gwamnatin Nyesom Wike ta dage cewa sai an binciki Rotimi Amaechi a kan zargin satar N96bn da yake Gwamna. Tsohon gwamnan ya je kotu, kuma ya samu aka tsaida binciken.
4. Hijabai a Makarantu
A 2014 ne wata kotu a Legas ta haramta amfani da Hijabai a makarantu, da aka je kotun koli a shekarar nan, an tabbatar da cewa babu dalilin da za a hana dalibai amfani da hijabi.
5. Peter Nwaoboshi
The Cable ta ce shari’ar Peter Nwaoboshi da EFCC na cikin wadanda za a tuna su a bana. An samu Sanatan da laifin satar N322m, jim kadan bayan an nemi a wanke shi daga laifuffukan.
6. Nnamdi Kanu
A Oktoban bana ne kotun daukaka kara tayi fatali da zargin ta’addancin da gwamnatin Najeriya take yi wa shugaban IPOB, Nnamdi Kanu. Sai dai hakan bai sa gwamnati ta fito da shi ba.
7. ‘Dan takaran Gwamna a gidan yari
Wata kotun tarayya ta yanke hukuncin daurin shekaru 42 ga Bassey Albert a dalilin satar motocin gwamnati. An yi hukuncin ne a lokacin da yake neman zama Gwamna a jam’iyyar YPP.
8. Doyin Okupe ya biya N13m
A karshe dole Doyin Okupe ya sauka daga kujerar Darektan yakin neman zaben Peter Obi bayan samun shi da laifi. A maimakon ya tafi kurkuku, Okupe ya biya gwamnati tarar N13m.
Shari’a 3 masu ban mamaki
9. IGP zai je kurkuku?
A baya an ji labarin yadda Mai shari’a Mobolaji Olajuwon ya zartar da hukuncin daurin watanni uku a gidan yari ga IGP Usman Alkali Baba saboda wani abin da ya faru tun a 1994.
10. An samu shugaban EFCC da laifi
Haka zalika a watan Nuwamban da ya wuce, Alkali Chizoba Oji ya yankewa shugaban EFCC na kasa, Mr. Abdulrasheed Bawa hukuncin dauri a gidan yari na Kuje saboda raina kotu.
11. Kotun Neja ta daure COAS
A ranar 1 ga watan Disamba, wata babban kotun jihar Neja ta samu shugaban hafsun sojojin kasa, Janar Faruk Yahaya da laifi, hakan ya jawo aka yanke masa hukuncin dauri a kurkuku.
Asali: Legit.ng