Hotuna: Mazauna FCT Sun Yi Shagalin Kirsimeti Tare da Shugaba Buhari
- Al'ummar Kiristoci mabiya addinin Kirista mazauna babban birnin tarayya sun kai wa Buhari ziyara a yayin shagalin Kirsimetin bana
- Sun samu jagorancin ministan babban birnin tarayya, Muhammad Bello, wanda ya kai su har cikin fadar shugaban kasan
- Sanata Smart Adeyemi tare da shugaban Kungiyar Kiristoci reshen FCT, Stephen Panyan, suna daga cikin wadanda suka kai wa Buhari ziyara
FCT, Abuja - Mazauna babban birnin tarayya dake Abuja a cikin ranakun karshen makon da ya gabata, sun yi shagalin bikin Kirsimeti da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja.
Wakilan da suka ziyarci Shugaba Buhari sun samu jagorancin Muhammad Bello, Ministan babban birnin tarayya dake Abuja, jaridar TheCable ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamai da Matasan Musulmi Sun je Coci, Sun Rarrabawa Kirista Kyautuka Don Inganta Alakar Zaman Lafiya a Kaduna
Kamar yadda Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter, a cikin su akwai Smart Adeyemi, shugaban kwamitin majalisa na FCT kuma Sanata mai wakiltar Kogi ta kudu tare da Stephen Panyan, mataimakin shugaban Kungiyar Kiristoci ta kasa, reshen babban birnin tarayya.
Ga Hotunan a kasa:
Musulmai sun kai wa Kiristoci ziyara a coci ranar Kirsimeti
A wani labari na daban, matasa da malamai mabiya addinin Musulunci a jihar Kaduna sun ziyarci Kiristoci a ranar shagalin bikin Kirsimeti ta bana.
Kamar yadda Fasto Yohanna Buru ya sanar, ba wannan bane karo na farko da suka samun ziyarar Musulmi ba duk don yakaka alakar dake tsakanin mabiya addinan biyu.
Yace hakan zai kawo hadin kai tare da ganin girman juna tunda ana mutunta addinan juna.
Buhari ya cika shekaru 80 a duniya
A cikin watan Disamban nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika shekaru 80 a duniya.
A ranar zagayowar ranar haihuwarsa, yana kan hanyarsa ta dawowa daga Amurka zuwa Najeriya inda matukan jirgin da yake da wasu mukarrabansa suka taya shi murna.
A hotunan da suka bayyana, an ga matukan jirgin sanye da kayan aiki inda Buhari ke zaune gabansa da kek wanda ya yanka.
Ban so shagalin zagayowar ranar haihuwata ba, Buhari
A wani labari na daban, shugaban kasan ya sanar da cewa bai son shagalin biki ranar zagayowar haihuwarsa ba, hakan ne yasa ya saka tafiyarsa a ranar.
ya mika godiyarsa ga ma'aikatansa da duk wadanda suka aike massa da kati ko sakonnin fatan alheri a wannan babbar ranar ta rayuwarsa.
Asali: Legit.ng