Jinin Sarauta Zalla: ‘Dan Sarkin Kano Zai Angwance da Kyakyawar Diyar Sarkin Bichi
- Gagarumin shagali da bidiri ne ke tunkaro masarautun Kanon Dabo da na Garin Bichi inda za a sha shagalin auren 'dan sarkin Kano da diyar sarkin Bichi
- Yarima Sanusi Aminu Bayero da Gimbiya Ummi Nasir ayero sun sasanta kansu kuma soyayya ta kullu inda ake dab da shafa fatiha
- Angon dai 'dan Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero ne, inda amaryar ta kasance diyar Mai Martaba Nasir Ado Bayero, Zakin gidan Dabo
Kano - Labari mai zafi dake zuwa a safiyar yau Lahadi shi ne na shirin shagalin auren jinin sarauta biyu da kuma zumunci, wanda za a yi a Kanon dabo.
Kyakyawan matashi mai kasaita, Yarima Sanusi Aminu Bayero zai angwance da zukekiyar budurwa mai aji, Gimbiya Ummi Nasir Bayero.
Yarima Sanusi Aminu Bayero 'da ne wurin Mai Martaba, Alhaji Aminu Ado Bayero, sarkin Kanon Dabo.
Ita kuwa Gimbiya Ummi Nasir Bayero, 'yar kwalisa, diya ce ga Mai Martaba, Alhaji Nasir Ado Bayero, sarkin Bichi kuma sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kamar yadda aka sani, bayan auren jinin sarauta zalla da wannan shagalin zai kasance, aure ne na dangi da zumunci tunda Mai Martaba Sarki Kano, Aminu Bayero, da Mai Martaba Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero, mahaifinsu da mahaifiyarsu daya.
Kamar yadda shafin @weddingcruize ya bayyana a wallafarsa:
"Wani auren jinin sarauta, kuma 'dan wa da 'yar kani ne auren. Yarima Sanusi Ado zai auri Ummi Nasir Ado Bayero. Mun kosa."
Sarkin Bichi ya ba Yusuf Buhari aure
A wani labari na daban, a shekarar 2021 da ta gabata ne Sarkin Bichi, Mai Martaba Alhaji Nasir Ado Bayero, ya aurar wa 'dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari, da diyarsa, Zahra Nasir Bayero.
Bikin da ya samu manyan baki daga sassan kasar nan daban-daban, an yi shi ne a watan Agustan 2021 kuma an daura shi afadar Mai Martaba sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero.
Kusoshin 'yan siyasa, hamshakan attajirai, 'yan kasuwa da masu fadi a ji daban-daban sun halarci wurin.
Gwamnonin jihohin Najeriya, ministocin Buhari da masu ruwa da tsaki a gwamnatinsa sun garzaya don taya 'dan shi namiji daya tilo murnar wannan ranar mai cike da tarihi a rayuwarsa.
Asali: Legit.ng