Osun: Shaida Ya Bayyana Yadda Gwamnan PDP Ya Samu Digiri Cikin Kwana 24
- Takkadar da ke tsakanin Gwamna Ademola Adeleke da tsohon gwamnan jihar Osun ta dauki sabon salo
- Hakan na zuwa ne a yayin da wani shaida ya bayyanawa kwamitin harkokin masarautu na jihar Osun yadda Adeleke ya samu digirinsa cikin kwana 24
- Shaidan ya ce ba digirin bogi Adeleke ke da shi ba kuma babu wani rashin daidaito a takardun karatunsa da ya mika don takarar zaben 16 ga watan Yuli
Ciyaman din kwamitin bita na harkokin masarautu na jihar Osun, Rabaran Samuel Bunmi Jenyo, wanda ya yi ikirarin cewa shi hadimi ne ga Gwamna Adeleke, ya ce gwamnan ya samu digiri dinsa cikin kwana 24.
Rabaran Jenyo ya ce Adeleke ya samu satifiket din Diplomansa daga Penn Foster High School a ranar 16 ga watan Yulin 2021 sai kuma digiri daga Atlanta Metropolitan College a ranar 9 ga watan Agustan 2021, The Nation ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jenyo ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 23 ga watan Disamba, yayin da ya ke bada shaida a gaban kwamitin sauraron kararraki ta Mai shari'a Tertsea Kume yayin da ake cigaba da sauraron shari'ar da tsohon gwamna Adegboyega Oyetola da APC ta shigar kan Ademola Adeleke a matsayin gwamnan jihar, kamar yadda rahoton This Day ya tabbatar.
Oyetola da APC na kalubalanta nasarar Gwamna Adeleke a kan dalilai biyu; kada kuri'u fiye da adadin wadanda aka tattance da kuma cancantarsa na yin takararsa saboda canje-canje a takardun karatunsa.
Jenyo ya nuna hujja, yana mai cewa Adeleke ba satifiket din bogi ya ke da shi ba
Rabaran Jenyo ya gabatar da takardun shaidan kammala karatu na Adeleke masu dauke da sunan Penn Foster High School da Atlanta Metropolitan State Collge.
Ya kuma fada wa kotun yayin amsa tambayoyi cewa duk da cewa bai taba aiki a makarantun da aka ce gwamnan ya yi karatu ba, daga cikin aikinsa a matsayin hadimi shine ajiye takardun gwamnan, hakan yasa ya ke da masaniya kan satifiket dinsa.
Kasa da awa 24 da hawansa kujerar gwamna, Adeleke ya kori ma'aikata 12,000 a Osun
A wani rahoton, Sanata Ademola Adeleke ya sallami ma'aikata 12,000 daga aiki ya kuma sauke sarakuna uku a Osun.
Ya aikata hakan ne kasa da sa'a 24 da hawansa kujerar gwamna kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Asali: Legit.ng