Yan Bindiga Sun Kashe Basarake, Sun Yi awon Gaba da Wasu Uku a Jihar Neja
- Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi ajalin Basarake a kauyen Mulo, karamar hukumar Mashegu a jihar Neja
- Kwamishinan tsaro da harkokin jin kai na jihar, Emmanuel Umar, ne ya tabbatar da haka yace lamarin ya faru ranar Alhamis
- Gwamna Abubakar Bello ya miƙa ta'aziyyar mutuwar Basaraken ya kuma umarci hukumomin tsaro su bazama nemo maharan
Niger - 'Yan bindigan daji sun kai farmaki ƙaramar hukumar Mashegu, jihar Neja, sun kashe Magajin gari a ƙauyen Mulo kuma sun yi garkuwa da wasu mutum uku.
Vanguard ta tattaro cewa yan bindigan sun yi wa basaraken, Alhaji Usman Garba, mummunan kisa kana suka watsar da gawarsa a kan Titi, suka yi awon gaba da mutanen uku.
Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin jin kai na jihar Neja, Emmanuel Umar, ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati dake Minna.
Kwamishinan yace lamarin ya auku ne ranar Alhamis da daddare. A cewarsa duk da an samu zaman lafiya a mafi yawan yankunan da ta'addanci ya shafa har yanzu akawai garuruwan da ke fuskantar barazana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Emmanuel ya ce a 'yan watannin da suka shige zaman lafiya ya fara dawowa amma garuruwa musamman Kontagora, Mashegu da Mariga na fama da barazanar harin 'yan ta'adda.
"An samu ci gaba sosai a ɓangaren tsaro a jihar Neja watanni kaɗan da suka shige amma akwai yankuna kalilan da har yanzun suke fama da barazana musamman Kontagora, Mashegu, da Mariga."
"Kwanan nan 'yan bindiga suka shiga wasu kauyuka a Mashegu ranar Alhamis, suka tasa mutane huɗu ciki har da Dagacin Mulo, Alhaji Usman Garba. Abin takaice maharan sun kashe Basaraken."
- Emmanuel Umar.
Wane mataki hukumomi suka ɗauka?
Yace gwamna Abubakar Sani Bello, ya yi ta'aziyyar mutuwar basaraken a madadin gwamnatin jihar Neja.
Haka zalika gwamnan ya umarci hukumomin tsaro su fantsama neman yan fashin jejin su ceto mutanen da suka sace kana su ragargaji sansanin 'yan ta'addan.
Kwamishinan tsaron ya yi kira ga ɗaukacin al'ummar kauyen su baiwa jami'an tsaro haɗin kai su taimaka masu ɗa bayanan sirri domin kawo karshen harin 'yan bindiga a yankunan.
A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun banka wuta a gidan Sarakuna da Jiga-jigan yan siyasa a jihar Anambra
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun banka wuta a gidan mataimakin kakakin majlisar jiha da Sarakunan garin Orsumoghu, ƙaramar hukumar Ihiala.
Baya ga haka, yan bindigan sun tafka ta'asa a harin, daga cikin gidajen da suka ƙona har da gidan shugaban al'ummar yankin, Nze Denis Muomaife.
Asali: Legit.ng