Yan Bindiga Sun Bankawa Gidan Mataimakin Shugaban Majalisa Wuta a Anambra

Yan Bindiga Sun Bankawa Gidan Mataimakin Shugaban Majalisa Wuta a Anambra

  • Yan bindiga sun kai wani kazamin hari garin Orsumoghu, karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra, sun tafka ta'adi
  • Maharan sun banka wuta a gidajen manyan mutane da ya haɗa da mataimakin kakakin majalisar dokokin jiha, Paschal Agbodike
  • Garin da lamarin ya faru na cikin yankunan da matsalar harin 'yan bindiga ya yi muni a kudancin Anambra

Anambra - Wasu miyagun 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun banka wuta a gidajen manyan mutane a ƙauyen Orsumoghu, ƙaramar hukumar Ihiala, jihar Anambra.

Vanguard ta rahoto cewa maharan sun cinna wuta a gidan mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Dakata Paschal Agbodike, mai wakiltar mazaɓar Ihiala II kuma ɗan takarar APGA a 2023.

Harin 'yan ta'adda.
Yan Bindiga Sun Bankawa Gidan Mataimakin Shugaban Majalisa Wuta a Anambra Hoto: vanguardngr
Asali: Twitter

Baya ga haka, yan bindigan sun tafka ta'asa a harin, daga cikin gidajen da suka ƙona har da gidan shugaban al'ummar yankin, Nze Denis Muomaife, da gidajen Sarakunan garin.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kaiwa Ayarin Dakarun Yan Sanda Hari a Arewa, An Rasa Rayuka

Garin Orsumoghu a shiyyar kudancin Anambra, tsawon shekara ɗaya kenan ya zama wuri mai haɗari ta yadda matafiya suka kaurace wa bi ta hanyoyin da suka haɗu da garin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tun da jimawa Direbobi suka daina bin babban Titin AwkaEtiti- Ukpor- Orsumoghu- Isekke, hanyar dake ɓulle wa zuwa jihar Imo da sauran jihohin kudu maso kudancin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigan sun jima suna gargaɗin jagororin al'umma a yankin, sun zarge su da ɗaukar nauyin kawo sojoji waɗanda suka hana su sakat suka fatattake su daga Dazukan garin.

Mazauna sun fara fargaba kasancewar lamarin ya faru ne a lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da babban zaɓen 2023 cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Bisa damuwa da rashin zaman lafiya, shugabar zaɓe a Anambra REC, Elizabeth Agwu, ta kira taron masu ruwa da tsaki na shiyyar Anambra ta kudu domin lalubo mafita.

Kara karanta wannan

Dubbannin Malaman Makaranta a Arewa Sun Yunkuro, Sun Ayyana Wanda Zasu Goyi Baya a 2023

Tuni dai shugabanni suka kafa kwamitin sulhu da zaman lafiya domin zama da matasan da suka cakuɗa tsaron shiyyar, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Gwamna Matawalle Ya Faɗi Gaskiyar Abinda Ya Faru Har Jirgin Soji Ya Kashe Mutane a Zamfara

A wani labarin kuma Gwamna Bello Matawalle ya tabbatar da kashe fararen hula yayin da jirgin soji ya biyo 'yan bindiga a Zamfara

A wani jawabin kai tsaye da ya yi, Matawalle yace gwamnatinsa zata tallafawa iyalan waɗanda suka mutu sakamakon kuskuren.

An cewa fararen hula da suka haɗa da mata da kananan yara 68 ne aka kashe, amma yan ta'adda sama da 200 sun sheƙa barzahu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel