Yan Sanda Sun Cafke Wani Saboda Murkushe Wani Da Mota Sakamakon Jayayya Da Suka Yi

Yan Sanda Sun Cafke Wani Saboda Murkushe Wani Da Mota Sakamakon Jayayya Da Suka Yi

  • Yan sanda a jihar Ogun sun kama wani mutum dan shekara 26 mai suna Adeyemi Babatunde kan zargin kisan kai
  • Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya take wani Obafunsho Ismail ne ta motarsa a lokacin da suke jayayya kan wani batu
  • Daga bisani wanda ake zargin ya fizgi motarsa ya tsere zuwa gidan mahaifinsa amma jami'an tsaro suka bi sahu suka kamo shi

Jihar Ogun - Rundunar yan sanda ta jihar Ogun ta ce ta kama wani Adeyemi Babatunde, dan shekara 26, kan kashe wani Obafunsho Ismail, dan shekara 46.

A cewar yan sandan, wanda ake zargin ya yi amfani da motarsa ya bige marigayin yayin jayayya da suka yi a ranar Talata, rahoton The Cable.

Wanda ake zargi
Yan Sanda Sun Cafke Wani Saboda Murkushe Wani Da Mota Sakamakon Jayayya Da Suka Yi. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Yadda jayayya ta kai ga halaka wani bawan Allah da mota

Kara karanta wannan

Elon Musk: Zan yi murabus daga shugabancin Twitter, amma ga sharadi daya

Abimbola Oyeyemi, kakakin yan sandan Ogun, cikin sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, ya ce an fara jayayyan ne bayan Babatunde ya yi amfani da motarsa ya bige Ismail, hakan ya lalata masa danja ta baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan hakan, an ce marigayin ya kusanci Babatunde ya bukaci ya sauka daga motarsa ya duba barnar da ya masa.

A cewar Oyeyemi, wanda ake zargin ya ki saukowa daga motarsa kuma ya yi kokarin tserewa.

Amma, an rahoto marigayin ya zauna a bayan motar wanda ake zargin don hana shi tserewa daga wurin.

Sanarwar ta ce:

"Wanda ake zargin, Adeyemi Babatunde, daga bisani ya sako ya gargadi marigayin ya sauka daga gaban motarsa idan baya son ya yi asarar ransa.
"Daga nan ya koma motarsa, ya figi motar da gudu hakan yasa marigayin ya fado daga motar kuma motar ta bi ta kansa.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kaiwa Ayarin Dakarun Yan Sanda Hari a Arewa, An Rasa Rayuka

"Bai gamsu ba, wanda ake zargin ya sake juyowa da motar ya bi ta kan marigayin don ya tabbatar ya mutu. Bayan kammala hakan, ya tsere da motarsa."

Yadda aka kama wanda ake zargin

Daga bisani an bi sahunsa an gano shi a gidan mahaifinsa a Kemta Idi a Abeokuta inda aka kama shi a ranar 20 ga watan Disamban 2022.

An kwato motar da aka yi amfani da shi wurin aikata laifin an kai ta caji ofis.

An kama gungun yan fashi da suka tafka barna a Abuja

A wani rahoton, yan sanda a birnin tarayya Abuja sun kama wata gungun yan fashi da ake zargin sune suka yi wa wani babban shagon magani fashi a unguwar Maitama.

Tunda farko, rahoto ya bayyana yadda yan ta'adda suka zo da muggan makamai shagon maganin tare da halaka wani mutum da ya nemi taka musu birki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164