'Yan Sanda Sun Dura Kan Gungun 'Yan Fashin Da Suka Yi Mummunan Barna a Abuja

'Yan Sanda Sun Dura Kan Gungun 'Yan Fashin Da Suka Yi Mummunan Barna a Abuja

  • Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya sun yi nasarar kame wani matashi da ake zargin ya yi fashi da makami
  • Tsageru sun kai farmaki wani shagon magani a Maitama, sun hallaka wani mutum tare da sace wata babbar mota
  • Ana yawan samun ayyukan barna a jihohi da sassan Najeriya, musamman a cikin 'yan shekarun nan

FCT, Abuja - Rundunar 'yan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta dura kan wani gungun 'yan ta'addan da ake zargin su suka yi fashi a wani shagon magani dake yankin Maitama a birnin tare da sace wata mota 'Prado'.

A baya rahoto ya bayyana yadda 'yan ta'adda suka zo da makamai tare da yin mummunan fashi a shagon maganin hadi da kashe wani mutum da ya yi kokarin kawo musu tsaiko a yunkurinsu na sace mutane.

Kara karanta wannan

An Rasa Ran Mutum 1 a Farmakin da ‘Yan Bindiga Suka kai Maitama Dake Abuja

Yadda aka kama daya daga 'yan fashin da suka kai farmaki shagon magani a Abuja
'Yan Sanda Sun Dura Kan Gungun 'Yan Fashin Da Suka Yi Mummunan Barna a Abuja | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yadda aka kama 'yan ta'addan

A ranar Alhamis 13 ga watan Oktoba, kwamishinan 'yan sandan FCT, Sunday Babaji ya gabatar da wani da ake zargin yana daga cikin wadanda suka aikata barnar, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babaji ya ce, an kama wanda ake zargin ne bayan wani kame da mai tsanani bayan samun bayanai da jami'an hukumar runtuma a Abuja.

Ya bayyana cewa, bayan da 'yan sanda suka shiga aiki kan lamarin, an tura jami'an sintiri da na dabaru domin tabbatar da tushen fashin.

A cewarsa, hakon 'yan sanda ya kai ga ruwa, domin bayan awanni bakwai da sace motar ta 'Prado', an gano ta a yankin Jabi Magajipi kusa da kwanar bankin Eco dake Jabi a Abuja.

Ya kuma shaida cewa, an kama wani Emmanuel Okoi da ake zargi yana da hannu a lamarin kuma mazaunin Jabi ne.

Kara karanta wannan

Wani Matashi Ɗan Najeriya Na Shirin Wuf da Wata Baturiya Da Suka Hadu A TikTok

Babaji ya kuma ce, ya umarci jami'ansa da kada su huta har sai sun kamo sauran wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.

Ya kuma tabbatarwa mazauna babban birnin tarayya cewa, hukumar za ta kara kwazo da kuzari wajen tabbatar da dakile munanan ayyukan ta'adda a babban birnin kasar.

An Kama Wasu 'Yan Jamhuriyar Kamaru 2 da Kokon Kan Dan-Adam a Jihar Adamawa

A wani labarin, jami'an 'yan sanda a jihar Adamawa sun kama wasu mutum biyu dauke da kokon kan dan adam da wasu kasusuwan da suka sato.

Hakazalika, rundunar ta kama wani da ake zargin shi zai sayi wadannan kayayyaki, Dauda Yakubu da aka ce mai sana'ar acaba ne da kuma wata mata da ake zargin tana da hannu a lamarin.

Mutanen biyu da aka kama sune Nodji Kodji da Raji Silver a kauyen Garware dake karamar hukumar Furore a jihar ta Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel