Cin Amanata Gwamnati Tayi, Shiyasa na Aurar da ‘Yan Matan FGC Yauri, Dogo Gide

Cin Amanata Gwamnati Tayi, Shiyasa na Aurar da ‘Yan Matan FGC Yauri, Dogo Gide

  • Gawurtaccen shugaban 'yan bindigar mai suna Dogo Gide ya ce dalilin da yasa yayi garkuwa da dalibai da malaman kwalejin gwamnati ta Yauri, shine don ya fusata gwamnati
  • A cewarsa, gwamnatin taci amanarsa saboda sun yi yarjejeniya amma ta karya alkawari, bayan ya taka babbar rawa wajen ganin an saki daliban da aka sace ba kwalejin kimiyya ta Kagara
  • Yayin da gwamnati ta masa alkawarin sakin masa mayakansa da ta kama, batun kudin fansa da ya bukata, ya ce masu sasanci tsakaninsu ne suka shawarce shi da ya bukata

Kebbi - Gawurtaccen 'dan bindigan nan, Dogo Gide, ya bayyana dalilin da yasa ya sace dalibai da malaman kwalejin gwamnati ta Birnin Yauri dake jihar Kebbi don ya fusata "gwamnati " ne bisa yadda ta karya alkawarin yarjejeniya.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Samu Gagarumar Nasara, Fitaccen Gwamnan APC a Arewa Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Amince da Bukatar PDP

Kwalejin Birnin Yauri
Cin Amanata Gwamnati Tayi, Shiyasa na Aurar da ‘Yan Matan FGC Yauri, Dogo Gide. Hoto daga Premiumtimesng.com
Asali: UGC

'Yan ta'adda sun auka makarantar a shekarar da ta gabata gami da yin garkuwa da sama da dalibai 90 da malamai. Yayin da gwamnatin jihar Kebbi ta ceto kusan duka wadanda aka sacen, wasu daga cikinsu run tsere daga sansanin.

Gide, wanda ya aurar da sauran 'yan mata 11 a sansaninsa, yayi magana ne a waya da kakakin dalibai, iyaye da marikan daliban FGC, Salim Kaoje.

Premium Times ta rahoto cewa, Gide ne ya auri kanwar Kaoje, Farida Kaoje.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abinda ya fusata ni, Dogo Gide

'Dan ta'addan, yayin magana da Kaoje bisa dalilin da yasa ya tsaya kan bakarsa na amsar kudin fansar N100 miliyan, ya ce yayi garkuwa da daliban ne don ya fusata gwamnati.

A cewarsa, "gwamnati" ta yaudare shi bayan ya taka babbar rawa wajen sakin yaran da aka yi garkuwa dasu a kwalejin kimiyya ta gwamnati dake Kagara jihar Neja.

Kara karanta wannan

Jarumta: Yadda budurwa ta lallasa 'yan bindiga masu AK47, ta ceto mutum 3 a hannunsu

Gide ya bayyana yadda ya taimakawa "gwamnati" yayin da wasu "barayi" suka sace daliban kwalejin gwamnatin kimiyya ta Kagara da yarjejeniyar za a sakar masa mayakansa da aka kama.

Premium Times ta rahoto cewa, ya tsaya kan cewa an yaudare shi saboda babu daya daga cikin mayakansa da aka sakI bayan taimakon da yayi wajen sakin daliban.

Daga bisani sai aka dinga kiransa da 'dan boko Haram.

A cewar Gide:

"Kai... kai ba ka san dalilin da yasa na sace wadannan yaran ba. Bari in fada maka dalilin da yasa na sace su tun farko. An ce min inyi kokarin ganin an saka daliban Kagara, ni kuma zasu sakar min mutane na da aka kama. Na bada umarnin a saki daliban Kagara, amma bayan nan, suka ci amanata gami da kin sakin ko daya daga cikin mutane na.
“Sun ce ni 'dan Boko Haram ne hakan ya harzukani. Na yanke shawarar kama mutanensu tare da cewa dole su sakarmin mutane kafin in sake su ( Daliban FGC Yauri)."

Kara karanta wannan

Leah Sharibu: Muna taimakawa Iyayenta, kuma ba zamu daina yunkurin ceto ba, Minista

Shugaban 'yan ta'addan ya ce, wasu daga cikin masu sasanci don ganin an saki yaran ne suka "lalata" komai, tare da bashi shawarar bukatar miliyoyin naira a matsayin kudin fansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng