Da Dumi-dumi: Emefiele Ya Sake Kin Amsa Gayyatar Majalisar Wakilai, Yan Majalisa Sun Dau Zafi

Da Dumi-dumi: Emefiele Ya Sake Kin Amsa Gayyatar Majalisar Wakilai, Yan Majalisa Sun Dau Zafi

  • Mambobin majalisar wakilai basu ga gwamnan CBN, Godwin Emefiele ba a ranar Tala, 20 ga watan Disamba
  • Ya kamata Emiefiele ya gurfana a gaban majalisar wakilai domin bayani a kan manufar takaita cire kudi da ya kafa a kwanan nan
  • Wannan shine karo na biyu da gwamnan babban bankin kasar ke kin bayyana a gaban yan majalisar

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya sake kin bayyana a gaban majalisar wakilai karo na biyu a ranar Talata, 20 ga watan Disamba.

Majalisar ta sammaci Emefiele domin yayi bayani kan sabon manufar babban bankin kasar ciki harda takaita yawan kudaden da mutum zai iya cirewa a bankuna, jaridar Punch ta rahoto.

Emefiele da Buhari
Da Dumi-dumi: Emefiele Ya Sake Kin Amsa Gayyatar Majalisar Wakilai, Yan Majalisa Sun Dau Zafi Hoto: @cenbank
Asali: Twitter

Majalisar Za ta yiwa Emefiele tambayoyi kan manufar a ranar Alhamis da ya gabata amma sai ya ki bayyana a gaban yan Majalisar.

Kara karanta wannan

Yan Takaran Jam'iyyar NNPP a Jihar Osun Sun Yi Watsi Da Kwankwaso, Sunce Tinubu Zasu yi

Mataimakin gwamnan na CBN, Edward Adamu, a wata wasika da ya aike majalisar, ya fada ma yan majalisar cewa Emefiele na cikin tawagar shugaban kasa Muhammadu Buhari da suka kai ziyarar aiki Amurka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mataimakin Kakakin majalisar wakilai, Ahmed Wase, wanda ya karanto wasikar a zauren majalisar a ranar Alhamis, ya ce Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, ya mayar da haduwarsu da Emefiele zuwa Talata.

Sai dai kuma, CBN ya sake aika wasika majalisa don fada masu cewa har yanzu Emefiele na kan aiki.

Majalisa ta yi martani

Gbajabiamila ya ce yan majalisar za su so sanin aikin da ya dauke shi tsawon makonni biyu, rahoton Daily Trust.

Shugaban marasa rinjaye, Ndudi Elumelu, ya bayyana cewa idan gwamnan na CBN ya ki bayyana a gaban majalisar a ranar Alhamis, lokacin da yan majalisar za su tafi hutun Kirsimeti da sabuwar shekara, kudirinsu na dakatar da manufar na nan.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Yan Bindiga Sun Harbe Shahararren Lauya a Babban Birnin Wata Jaha

Kotu ta yi watsi bukatar kama gwamnan CBN

A wani labarin, wata babbar kotu a babban birnin tarayya Abuja ta yi watsi da bukatar hukumar DSS na neman izinin kama gwamnan babban bankin Najeriya.

Kamar yadda aka rahoto, ana neman umurnin kama Emefiele ne kan harkarlar kudade, zamba da kuma tabarbarar da harkokin tattalin arzikin kasar.

Mai shari'a John Tsoho ya ce abun da DSS ta nema bai kai a bata hurumin kama gwamnan babban bankin kasar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng