Yadda Ake Bambance Sabbin Takardun Naira Na Bogi da Na Gaske

Yadda Ake Bambance Sabbin Takardun Naira Na Bogi da Na Gaske

  • Kwanaki kadan bayan kaddamar da sabbin takardun Naira, tuni kudaden bogi masu kama da sabbin kudin suka fara yawo a Najeriya
  • Yana da matukar kyau ka kare kanka daga fadawa hannun macuta da ka iya ba ka sabon kudin bogi da ke yawo a madadin sahihi
  • Legit.ng Hausa ta tattaro muku abubuwan da ya kamata ku maida hankali a kai wajen gane sabon kudin bogi da na gaske

Tun bayan da babban bankin Najeriya ya sanar da fara kashe sabon kudin da ya sauyawa fasali aka samu bata-garin da ke ba mutane kudaden bogi a Najeriya, mutane da yawa sun fada hannun macuta.

Sai dai, a nasa bangaren, babban bankin CBN ya ce akwai wasu maganadisun kariya da ke jikin sabbin kudaden da aka yi, wadanda da gani babu tambaya, mai lura zai fayyace na bogi da na gaske.

Kara karanta wannan

A zauna lafiya: Hotuna yadda wata mata Musulma ta raba kudi, abinci da atamfa ga kiristocin Kaduna

Kadan daga abubuwan da za a iya cewa su ne bambancin, wasu abubuwa ne da ke da alaka da layin jikin kudin mai launin farin karfe da kuma rubutun sarkafe da ke kwance a jikin kudin.

Yadda ake bambance kudin gaske da na bogi
Yadda Ake Bambance Sabbin Takardun Naira Na Bogi da Na Gaske | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

Don kare 'yan Najeriya daga fadawa asara, Legit.ng Hausa ta tattaro muku abubuwan da ya kamata ku maida hankali don gane na bogi da na gaske.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

1. Lura da sahihin siririn layin da ke jikin kudin

Don gane kudin bogi ko na gaske, duba wani siririn layi da ke jikin kudin; daga sama har kasa. Wannan layin da aka shinfida a jikin kudin ana samunta ne a jikin kudin gaske kadai.

Kudin bogi ba zai zama yana da wannan siririn layi ba, sai dai kamanceceniya da karara zai nuna na bogi ne; daga launin da zubin.

2. Lura da tsarmin zinare a jikin kudin

Kara karanta wannan

Sabbin Kudi: An Damfari Wani Mai Sana'ar Da KUma Hada - Hadar Banki Da N1000 Sabbi

A bangaren dama na kudin Najeriya, akwai wata alama da aka yi da tsarmin zinare, daidai gefen sa hannun gwamnan CBN.

Za ku iya gane kudin bogi ta hanyar lura da wannan alamar. Idan kuka iya kankare wannan alama ta zinare, tabbas wannan na nufin kudin na bogi ne; na gaske bai iya kankaruwa.

3. Lura da ingancin takardar

Takardun kudi ba takardu ne gama-gari da ake amfani dasu ba, ana yinsu ne daga wani nau'in takarda na musamman, kudin bogi kuwa da takarda gama-gari ake yinsu, za ku iya gwadawa.

Idan a hannunka a yanzu kana da kudin gaske da wanda kake zargin na bogi ne, ka rige su daya a hannun dama daya a hagu.

Yanayin karfi da ingancin takardar kudin gaske ya bambanta da na bogin da ke hannunka, daga rike wa za ka gane takardar kudi da ta kasuwa gama-gari.

4. Lura da ingancin launin da aka yi kudin

Kara karanta wannan

Kudin makamai: Tashin hankali ga dan takarar shugaban kasa, kotu ta daure jigon kamfen dinsa

Zane-zane da launikan jikin kudin gaske ba masu gogewa bane, na dindindin ne kuma garau suke, yayin da na bogi kuwa sun kasance dishi-dishi sannan za su iya gogewa, ya danganta da kwarewar mai buga na bogin.

A lokuta da dama, launi da zanen kudin bogi na iya gogewa cikin sauki da zarar sun sha 'yar matsa kadan.

5. Zuba ruwa ko dangin abu a jikin kudin

Idan kuna shakkar kudin da aka baku, tsoma su a ruwa ko man fetur sannan ku wanke da hannu ku sha mamaki. Idan kudin bogi ne, launikan da ke jikinsu zai dishashe ya tafi, kamar dai launikan wasan yara na makaranta.

Idan kuma na gaske ne, daram za ku ga bai goge ba, sannan launin bai zuba ba.

6. Gwada amfani da kwan haske na mercury

Hanya mafi inganci wajen bambance kudin bogi da na gaske shine ta amfani da kwan haske 'mercury'.

Kara karanta wannan

Wata Mata Tace Allah-Fa-Fir Bazata Karbi Sabon Kudi Ba, Sabida Jabu Ne

Akwai wasu surkullen da aka lakkaba a jikin kudi ba ido bai iya ganinsu, sai da taimakon wasu abubuwan gani na zamani.

Kwan haske na 'mercury' na iya gani irin wadannan surkulle da ke boye ba tare da wata-wata ba, idan da dama, ku gwada amfani dashi.

Irin wadannan surkulle da ke jikin kudi ba abu ne mai sauki da za a iya kwafewa ko kwaikwaya ba, don haka kudin gaske ta nan ya tsira daga kwafin masu buga kudin bogi.

Idan kuka saka kudin da kuke shakkar ingancinsu a hasken kwan 'mercury', za ku iya ganin wasu rubuce-rubuce a boye a jikin kudin gaske; sabanin na bogi.

Sai jama'a suke kulawa, domin an damfari wani mai hada-hadar kudi a Najeriya, inaga jama'a gama-gari?

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.