Amarya Ta Tubure Tace Bata Yi a Ranar Da Za Daura Mata Aure Da Angonta
- Ranar da ya kamata ace ya zama na fatin ciki ga wasu masoya ya zama na bakin ciki sakamakon abun da amaryar ta aikata
- Mai shirin zama amaryar ta tubure tace bata auren angonta lamarin da ya haddasa cece-kuce a coci
- Jama'a sun yi martani a kan batun bayan cin karo da bidiyon wanda wani da ya halarci bikin ya dauka
Wata amarya yar Najeriya ta ki yarda ta auri angonta a lokacin da ake gab da daura masu aure a coci.
Wani da ya halarci daurin auren ne ya nadi bidiyon abun da ya faru mai cike da ban mamaki sannan ya wallafa a TikTok. Lamarin ya kuma ja hankalin mutane da dama.
Bidiyon da aka dauka daga nesa ya nuno amaryar tsaye kusa da angon tana kallo cike da rudu a gaban limamin cocin da zai daura masu auren.
Faston ya lura da yanayinta kuma hakan yasa ya tambayi amaryar ko ta shirya ma auren.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga mamakin mutane, sai amaryar ta amsa tambayar faston da a'a. Hakan ya haifar da rudani a cikin taron.
Faston ya yi kokari wajen kwantar da hayaniya a tsakanin bakin da suka hallara a wajen.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
use @oriade_kindlove ta ce:
"Me yasa ta bari gayen ya shirya ma auren kafin wannan rana....ita ta san abun da ke faruwa."
D’mmyReflect ta ce:
"Akwai wani gaye da na shirya yi ma irin wannan abun...amma wani ya bani shawara shine yasa na kyale shi na tabbata tana da dalilinta."
ajokeade851 ta ce:
"Baaba akwai rina a kaba watakila angon ya yi mata laifi ko kuma yan kauyensu na binta."
La gaff ya ce:
"Asiri ya kare a coci."
osazeeomoruyi130 ta ce:
"Yar ruwa. Aljanin mijinra ya hallara kuma ya sa ta ki amincewa da aurensa...
"Kada ku yi shakku a kaina dan Allah."
Iyali sun garzaya wajen biki harda anko, sun tarar ba ranar bane auren sai watan gobe
A wani labari, wani iyali sun kunshi takaici bayan sun yi tattaki daga Lagas zuwa jihar Osun da nufin halartan wani daurin aure.
Bayan sun isa wajen sanye da anko, sai ake fada masu ba ranar bane bikin sai wata mai kamawa.
Asali: Legit.ng