Jihohin Da Za'a Iya Samun Tashin - Tashina A Lokacin Babban Zaben 2023

Jihohin Da Za'a Iya Samun Tashin - Tashina A Lokacin Babban Zaben 2023

  • Zaben shekarar 2023 a Nigeria kan iya zuwa da matsala sabida yadda wasu dai-daikun mutane ke aikata aiyukna barazana a yankunan
  • 'Yan awaren Biafra, Boko Haram da kuma masu aikata garkuwwa da mutane sune manyan irin aiyukan da akeyi a yankin arewa maso yamma, kudu maso gabas da kuma arewa maso gabashin kasar nan
  • Wasu abubuwan da ake ganin kan iya rurar wutar rikincin zabe sun hada da yadda ake tinzura magoya baya akan abubuwan da suka shafi zaben

Gabanin babban zaben shekarar 2023 da yake kan kwana, matsalar tsaro na kara kamari a wasu jihohi, wanda hakan kan iya kawo cikas din zaben.

Yanayin rashin tsaron da ake fama da shi a Nigeria sun hada da na 'Yan awaren Biafra a yankin kudu maso gabashin kasar nan, da rikicin 'yan Boko Haram da 'yan garkuwa da mutane a yankin gabashi da kuma ymmacin arewar kasar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Yan Bindiga Sun Harbe Shahararren Lauya a Babban Birnin Wata Jaha

Wasu kanannan rikicin da ake ganin suma zasu iya rura wutar sun hada rikicin manoma da makiyaya, rikicin kabilanci a tsakiyar Nigeria wato arewa ta tsakiya.

Masana harkokin siyasa sun fitar da wasu yankuna da jihohi da suke tunanin za'a samu tashin-tsahina a lokacin zabe.

Kudu Maso Gabashin Kasar Nan

Akwai kura babba musamman ma a jihohin da 'yan awaren Biafra suke da tasiri ko karfi wanda suka hada Enugu, Abia, Imo, da kuma Anambra, sune a gaba-gaba da ake ganin za'a iya samun babbar matsala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lagos

Cinkus dakin tsumma kirarin da ake mata kenan, ana ganin ita ma za'a iya samun tashin tashina a cikinta, sabida yadda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed ya fito daga jihar kuma da yadda dan takarar jam'iyyar LP ke zaune a jihar.

Kara karanta wannan

Tsohuwar Abokiyar Gabar Bola Tinubu Ta Bayyana Halin Lafiyar ‘Dan Takaran APC

Ana ganin yadda magoya bayan Tinubu da Obin kan nunawa juna yatsa, da gatsine dan gane da kare muradinsu, musamman ma a yankunan da ake ganin Inyamurai sun mamaye wajen.

Magoya Baya
Jihohin Da Za'a Iya Samun Tashin - Tashina A Lokacin Babban Zaben 2023 Hoto: Nigerian Police
Asali: UGC

Kaduna, Katsina, Sokoto da Zamfara

Jihohin arewa maso yamma na fama da rikicin masu garkuwa da mutane musamman ma a jihohin Sokoto, Kebbi, Zamfara da Sokoto.

Da yawa daga cikin kauyukan wannan jihihohin sun zama kango, sakamakon yadda aiyukan yan tada kayar bayan suka tashesu.

Kano

Ana ganin jihar Kano a matsayin Giwa sabida yadda ake mata kallon madubi ga siyasar Nigeria ko arewacin kasar nan. Kuma jihar tana karkashin jam'iyyar APC ga kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a jihar.

Hakan na barazana ga zaben, musamman ma yadda aka jiyo shugaban jam'iyya mai muki a jihar ke magana kan batun zaben.

Benue, Plateau da Taraba

Kara karanta wannan

Enugu: ‘Yan Sanda Sun Kakkabo ‘Yan Ta’adda, Sun Cafke 4 da Miyagun Makamai

Wadannan jihohin sunyi kaurin suna wajen rikicin kabilanci da kuma addinai da ake tunanin kuma hakan kan iya shafar zaman lafiyar jihohin a lokacin zabe.

Borno

Aiyukan kungiyar ta'addancin ta Boko Haram ya ragu a yankin, to amma yadda aka ga an kaiwa dan takarar jam'iyyar PDP hari wani batu ne da ace an duba shi.

Ana ganin za'ai taho mu gama da magoya bayan jam'iyyar PDP da APC, duba da yadda jihar jam'iyyar PDP bata taba ci ba tun bayan dawowa daga dimukuradiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida