Sai Gudu Kake Ina Zaka Je? Hadimin Atiku Abubakar Yana Yiwa Tinubu Isgili
- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya wani kakkausan martani ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC.
- Mai taimakawa Atiku, Phrank Shu'aibu ya nunawa dan takarar shugaban kasa na APC Bola Ahmed Tinubu yatsa kan kin tsayawarsa a muhawarorin da aka shirya tsakaninsa da takwarorinsa.
- Gabanin zaben shekarar 2023, mai taimakawa Atiku yace, Atiku ne kadai zai iya amma ba mai gujewa muhawarar yan takara ba wato Tinubu, kamar yadda yake tambayarsa.
ABUJA: Phrank Shu'aibu mai taimakawa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubkar ya jefawa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu kalubale dan gane da rashin zuwansa tarukan muhawara da 'yan takarkari.
A wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi, Shu'aibu yace ya jefa kalubale ga dan takarar shugaban kasa na APC kan shekarunsa, tarihinsa da kuma ahlinsa. Kamar yadda Shu'aibun ke ganin sune ke hana shi zuwa muhawarorin.
Mai Taimkawa Atiku Ya Bayyana Abu Da Dan Takarar APC Ke Boyewa
A ranar 5 ga watan Disambar nan, tsohon gwamnan jihar Legas din yace shi tarinhinsa cikakke ne kuma kammallele a "CHATHAM HOUSE" dake Londan.
Shu'aibu yace tarihin Atiku ba wai boyayyan batu bane kuma ba kokwanto akan tarihin nasa kamar yadda na Tinubu ya zama kila wa kala.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yayin da ake batun shin tarihin Tinubun ya cika ko bai cika ba, Shu'aibu yace mai "Bola" ta ke a sunan Tinubu, kamar yadda jaridar The Cable ta rawaito
"Marar gaskiya ko a ruwa gumi yake, amma shi kwa mai gaskiya wuka bata huda cikinsa kamar yadda littafi mai tsarki yace
"Wannan dalilin ne yasa Tinubu baya iya halartar tarukan muhawara sai da ya tura wakili, ko kuma yaki halartar tarun kai tsaye da gidajen jaridu suke shirya kon wasu kungiyoyi"
"A shekerar 2007 shugaban ma'aikatan jihar Legas, Abdul-Ra'uf Babatunde Tinubu wani dattijo a ahlin su Tinubu ya wallafa wani littafi mai take "Onijumu Wura: Zuri'ar gidan Kakaka (Tasawirar ahli)"
"Wanda ya buga littafin ya bayyana cewa duk wanda sunan sa baya cikin wannan littafin to ba dan zuri'ar Tinubu bane.
Daga ina Tinu yake? Su waye iyayensa ? Mainene cikakken sunan Tinubu? Shin Bolitito ne, ko kuma Abolaji Bilawarin?
..... Shu'aibu yake tambaya
Ya kamatawa a cirewa 'yan kasa wannan shakkun da ya dabaibaye dan takarar nan sabida ka aje a sa Nigeria a yankan shakku.
Ba Dole Sai Tinubu Ya Halrci Taron Muhawara Da 'yan Takarkari Ba.
Kakakin yakin neman dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, yace ba zama dole ace sai dan takarar tasu ya halarci muhawara da yan takarakari ba.
Kakakin wannan batun ne a lokacin da yake maida martani ga wani rahotan da gidan talabijin na Arise Tv ta fitar.
Asali: Legit.ng