ICPC Zata Daukaka Kara aka Wanke Hadimin Gwamna da Kotu Tayi kan Mallakar Gidaje 220
- Hukumar yaki rashawa da laifukan da Makama yan hakan (ICPC) ta lashi takobin daukaka kara game da hukuncin da kotu ta yanke ga tsohin hadimin gwamna Isa Yuguda
- Hakan ya biyo bayan maka hadimin kotu kan mallakar gidaje 220 a rukunnan gidaje 20 a Bauchi ba bisa ka'ida ba wadanda sun kai kimar N1,857,351,750
- Kotu ta tuhumesa da jerin laifuka 36 daga bisani ta wankesa gami da umartar hukumar da ta sakar masa kadarorinsa ya tafi abin shi
Hukumar yaki da rashawa da sauran laifuka da makamantan hakan (ICPC) ta ce zata daukaka kara a kan hukuncin da kotu tayi kwanan nan ga Sanusi Muhammad, hadimin tsohon Gwamnan Bauchi.
Azuka Ogugua, kakakin ICPC ya bayyana hakan a wata takarda da ya fita ranar Lahadi.
Muhammad hadimi ne na musamman ga Isa Yuguda tsakanin 2007 zuwa 2016 yayin da Yuguda yake gwamnan jihar Bauchi.
Premium Times ta rahoto cewa, a 2017, ICPC ta bankado gami da kwace gidajen hadimin guda 220 dake rukunnan gidaje 20 a Bauchi, wadanda zasu kai kimar N1,857,351,750.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga bisani aka gurfanar da Muhammad a babbar kotun jihar Bauchi inda aka tuhumesa da laifuka 36 da suka shafi rashawa, jaridar TheCable ta rahoto.
A ranar Talata, Rabi Umar, alkali mai shari'a, ta sallama gami da wanke Muhammad bisa laifukan da ake tuhumarsa dasu sannan ta umarci hukumar da ta sakar masa kadarorinsa.
Martanin ICPC
Yayin martani game da lamarin, ICPC ta ce hukuncin da aka yanke:
”ba a gabatarwa kotu da gamsassun hujjoji ba."
Hukumar yaki da rashawar ta ce kadarorin da ta kwace daga wanda ake karar:
"sun siye su ne da kudin jihar kuma shi kawai ya tsaya ne a gaban wani 'dan siyasa wannan ne wanda shine mamallakin haramtattun kadarorin."
"Wasu daga cikin hujjojin da aka gabatarwa kotu sun nuna cewa wanda ake karar ba zai iya mallakar gidaje masu dakuna biyu guda 220 da masu dakuna uku ba, wadanda ke rukunnan gidaje 20 da sauran kadarori da albashinsa da alawus ba. Gidaje 220 a rukunnan gidaje 20 din sun kai kimar N1,857,351,750.”
- Kamar yadda takardar ta bayyana.
"Sanusi Muhammad Isa yayi aiki ne da Bauchi Investment Corporation daga 3 ga watan Oktoba, zuwa 31 Disamba, 2012 kafin komawarsa ofishin shugaban ma'aikatan jihar Bauchi a ranar 31 Disamba, 2012 a matsayin darakta a mataki na 16.
"An nada Isa a matsayin hadimi na musamman ga tsohon gwamnan jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda a ranar 22 ga watan Disamba, 2008.
"A aikin da yayi a matsayin hadimi na musamman ga gwamnan, yana morar albashin da wasu alawus na N9,122,388.45 duk shekara ga Bauchi Investment Corporation, sannan yana samun alawus na N15,000.00 daga tsohon gwamnan."
Ban tsere ba, karaya na samu: Maina a Kotu
A wani labari na daban, rashin bayyana Abdulrasheed Maina a kotu har sau uku ta tayarwa Sanata Ndume hankali.
Sai dai daga bisani ya bayyana a bidiyo inda ya sanar da cewa yana asibiti ne ba tserewa yayi ba.
Asali: Legit.ng