Ba guduwa nayi ba, na samu karaya ne a gwiwa: AbdulRashid Maina ya bayyana
- AbdulRasheed Maina ya ki zuwa kotu har sau uku kamar yadda Alkali ya bukaci ganinsa
- Bacewar Maina ya tayarwa Sanata Ali Ndume hankali saboda shi ya tsaya masa a kotu
- Maina ya bayyana a sabon bidiyo inda yace ba guduwa yayi ba, yana asibiti ne
Tsohon shugaban kwamitin gyara harkan fansho, Abdulrasheed Maina, ya bayyana bayan zaman kotu kimanin uku an nemeshi an rasa.
A bidiyon da TVCNews ta wallafa, ana iya ganin AbdulRasheed Maina kwance kan gado da dauri irin da wanda ya samu karaya kuma yaronsa Faisal na zaune gefensa.
Ya bayyanawa dan jaridan dake hira da shi cewa Alkalin kotun ba ya son sa gaba daya kuma hakan ya nuna cewa wasu na son ganin bayansa.
Ya bayyana cewa ba guduwa yake ba, halin da ya samu kansa ne a yanzu.
"Ina kwance ina jinya gwiwa, ba guduwa nike daga kotu ba" Yace
DUBA NAN: Malaman Jami'a: Duk wanda baiyi rijista a IPPIS ba bai da rabo a kasafin kudin 2021 - Buhari
KU KARANTA: Tattalin arzikin Najeriya zai iya 'komawa gidan jiya' a karo na biyu cikin shekaru 4 - Buhari
Bacewar Maina ya saka wanda ya tsaya masa a kotu, Sanata Ali Ndume, fuskantar matsin lamba na neman soke lamunin da yayi masa.
Maina, dansa da kamfanin Common Input Property and Investment Ltd na fuskantar shari’a a gaban Okon Abang na babbar kotun tarayya, Abuja kan zargin zambar kudi naira biliyan biyu.
An gurfanar da su kan tuhume-tuhume 12 da suka hada da damfara da sauransu.
Koda dai Sanata Ndume ya hallara a kotu, wanda ake zargin ya ki zuwa kotu a ranakun Juma’a, Litinin da Talata da suka gabata.
An tattaro cewa magana ta karshe da aka yi da Maina ya kasance a daren ranar Alhamis, lokacin da ya sanar da cewar zai halarci zaman kotu a ranar Juma’a da ta gabata.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng