Bayan Wata 6, Sojin Sama Sun Ceto ‘Yan Chana 7 Daga Masu Garkuwa da Mutane

Bayan Wata 6, Sojin Sama Sun Ceto ‘Yan Chana 7 Daga Masu Garkuwa da Mutane

  • Dakarun sojin saman Najeriya karkashin shiyya ta 271 a Birnin Gwari dake Kaduna sun ceto 'yan China bakwai da aka sace a jihar Neja
  • Hakan ya biyo bayan sace su da aka yi watanni shida da suka wuce a mahakar ma'adanai cikin Ajata-Aboki na gundumar Gurmana karamar hukumar Shiroro
  • Tsananin luguden wutar da sojin saman Najeriya suka musu ne ya tilasta 'yan ta'addan tserewa gami da watsi da makamansu da sauran abubuwan don tsira da ruyuwarsu

Kaduna - Dakarun sojin saman Najeriya na musamman karkashin shiyya ta 271 na Birnin Gwari a jihar Kaduna, sun ceto 'yan China bakwai da masu garkuwa da mutane suka sace a jihar Neja.

Dakarun NAF
Bayan Wata 6, Sojin Sama Sun Ceto ‘Yan Chana 7 Daga Masu Garkuwa da Mutane. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

An yi garkuwa da bakin hauren ne a watan Yuni yayin aiki a mahakar ma'adanai, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Harbe Daraktan Kwamitin Kamfen Atiku A Wata Jiha

Daraktan yada labarai na sojin saman Najeriya, Air Commondore Edward Gabkwet ya bayyana a wata takarda da ya fita ranar Asabar yadda aka cetosu bayan jami'an sun aiwatar da wani aikin bincike da ceto.

Takardar ta bayyana:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Rundunar sojin saman Najeriya na Birnin Gwari karkashin shiyya ta 271 dake Kaduna, ta aiwatar da wani aiki na ceto a safiyar ranar 17 ga watan Disamba, 2022 wanda yayi sanadiyyar ceto 'yan China bakwai da 'yan ta'adda suka yi garkuwa dasu.
"’Yan Chinan da aka ceto daga hannun masu garkuwa da mutane sune wadanda aka yi garkuwa dasu a Yunin 2022 yayin aiki a mahakar ma'adanai cikin Ajata-Aboki na gundumar Gurmana ta karamar hukumar Shiroro dake jihar Neja.
"Tawagar jami'an tsaron sintiri da ceton ta kunshi dakaru 35, wacce aka gabatar a cikin dare a Kanfani Doka da yankin Gwaska wanda ya tilasta 'yan ta'addan watsi da makamansu da kayayyaki da kuma 'yan Chinan da suka yi garkuwan dasu. 'Yan ta'addan sun ranta ana kare don tsira da rayukansu saboda irin luguden wutar da suka ji daga dakarun."

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Halaka Abu Na-Iraqi da Abu-Na Masari, Gawurtattun 'Yan Ta'addan da Suka Addabi Katsina

Gabkwet ya kara da cewa, an gaggauta garzayawa da wadanda akayi garkuwan dasu asibitin NAF na shiyya ta 271 don duba lafiyarsu, sannan an tabbar da lafiyar biyu da ciki.

A cewarsa, duka bakwan da aka yi garkuwa dasu suna asibitin NAF na Kaduna don cigaba da binciken lafiyar su.

Yan bindiga sun rufe titin Gusau zuwa Dansadau

A wani labari na daban, wasu tsagerun ‘yan bindiga sun kai farmaki babban titin Gusau zuwa Dansadau inda suka hari fasinjoji.

Kamar yadda aka gano, harin daukar fansa ne da suka kai wa jama’a bayan ‘yan sa kai sun halaka 15 a cikinsu a farmakin da suka kai Maigoge.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng