Mutane da Yawa Sun Mutu Bayan Cin Abinci Mai Guba a Jihar Kuros Riba
- Ana fargabar mutane da yawa sun mutu a garin Ekureku da ke karamar hukumar Abi a jihar Kuros Riba
- Al'ummar da lamarin ya shafa sune; Agbara, Ngarabe, Ekureku-be, Akpoha, Akare-for, Anong, Amenekpon da dai sauransu
- Rahotanni sun bayyana cewa, mutanen yankin na fama da tashin hankalin rashin ruwan sha mai tsafta na tsawon lokaci
Ana fargabar mutane da yawa sun mutu a karamar hukumar Abi ta jihar Kuros Riba bayan cin abinci mai guba.
Sakataren dindindin na ma'aikatar lafiya ta jihar Kuros Riba, Dr Iwara Iwara ya tabbatar faruwar lamarin ga kafar labarai ta Channels Tv a ranar Asabar 17 ga watan Disamba.
Ya bayyana cewa, jami'an taimakon gaggawa ciki har da na Red Cross da na hukumar yaki da annoba da ma'aiukatar lafiya sun tafi ga jama'ar karamar hukumar don tabbatar ceto jama'a da kuma gano tushen gubar.
Inda ake kyautata zaton cutar ta samo asali, da yadda ta kashe mutane da yawa a kauye
Jaridar Vangurda ta ruwaito cewa, cutar kwalara ce ta barke, ta yi sanadiyyar mutane 30 nan take a wadannan yankuna.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar jaridar, wadannan wuraren da aka lissafa gaba dayansu suna wani yanki ne da ke da iyaka da jihar Ebonyi, mai makwabtaka da jihar ta Kuros Riba.
A bangare guda, an ce barkewar cutar ta kwalara dai bata fi kwanaki biyu, inda mazauna kauyukan suka fara barkewa da zawo da amai ba gaira ba dalili.
Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta sha bayyana cewa, yana dai kyau mutane suke kulawa da lafiyar abinci da abin sha, musamman a irin wannan lokaci da ake yawan samun barkewar cututtuka.
Ba wannan ne karon farko da mutane ke mutuwa sanadiyyar mummunar annobar da ta barke a yankuna ba, an sha samun irin wadannan matsaloli a yankuna daban-daban na kasar nan.
Cutar kwalara ta barke a Abuja, mutane 604 sun kamu, 54 sun riga mu gidan gaskiya
A babban birnin tarayya Abuja, akalla mutane sama da 54 ne suka riga mu gidan gaskiya bayan da wutar kwalara ta barke.
Hakazalika, rahoton da muka samo ya ce akalla mutane 604 ne suka kwanta a asibiti bayan da aka samu barkewar cutar.
Hukumomin lafiya na ci gaba da kai komo don ganin an shawo kan irinwannan matsala.
Asali: Legit.ng