'Yan Bindiga Sun Bankawa Babbar Kotun Jihar Imo Wuta, Sun Tafka Ta'asa
- Wasu miyagun 'yan bindiga sun banka wuta a ginin babbar Kotun jihar Imo da ke Orlu da safiyar Asabar
- Hakan ta faru ne kwanaki kaɗan bayan wasu tsageru sun ƙona ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC na Owerri
- Hukumar yan sanda reshen jihar Imo ta tabbatar za kai harin Kotu, tace tuni jami'ai suka kaddamar da bincike
Imo - Rahoton da muka samu da safiyar Asabar ɗin nan ya nuna cewa 'yan bindiga sun bankawa ginin babbar Kotun jihar Imo wuta, an ce wutar ta kone sashin da ake ajiyar takardu masu muhimmanci.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu miyagu sun farmaki Hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ke Owerri, babban birnin Imo, wanda 'yan sanda suka ɗora kan 'yan aware IPOB.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ɓangaren da wutar ta shafa na ƙunshe da fayil-fayin da takardun babbar Kotun da kuma na Kotun Majistire.
Wani ma'aikacin ɓangaren shari'a, wanda ya zanta da wakilin jarida bisa sharaɗin boye sunansa, ya ce baki ɗaya fayil-fayin ɗin Kotun sun ƙone kurmus.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Legit.ng Hausa ta gano cewa babbar kotun da ke Orlu na kusa da shingen binciken ababen hawa na jami'an tsaro kuma kusa da Caji Ofis ɗin 'yan sanda a yankin.
A shekarar 2018, wasu miyagu suka babbake Kotun haka zalika a ranar 1 ga watan Disamba aka sake ƙone Ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC da ke Orlu.
Shugaban ƙungiyar lauyoyi reshen Orlu, (NBA), Barnabas Munonye, wanda ya tabbatar da harin yau Asabar, yace bai kamata ace irin haka na faruwa ba.
Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Imo, CSP Mike Abattam, wanda ya tabbatar da lamarin yace tuni jami'an yan sanda suka fara bincike.
A wani labarin kuma kun ji cewa an Sake Samun Fashewa Babbar Tanka a Babban Birnin Jihar Oyo
Tankar dakon Man fetur ɗin wacce aka ce ta sha karfin direban, ta yi kan wasu shaguna a gefen titi kana ta fashe kuma ta kama da wuta.
Wani Bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda wuta ta kama rigi-rigi yayin da waɗanda suka ga faruwar lamarin suka soma kururuwar neman a kawo ɗauki.
Asali: Legit.ng