Darusa 10 da Za a Dauka daga Shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara – Kabir Asgar

Darusa 10 da Za a Dauka daga Shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara – Kabir Asgar

Dr. Asgar wanda malamin addinin musulunci ne a garin Zaria, shi ya yi wannan rubutu. Abin da yake ciki, ra’ayinsa ne ba na Legit.ng Hausa.

  • A wani rubutu da ya yi a shafinsa, Dr. Kabir Asgar ya zakulo wasu abubuwan lura daga shari'ar Abduljabbar Nasiru Kabara a kan zargin batanci
  • Malamin yake cewa wasu daga cikin fa'idojin da za a iya tsinkaya shi ne cika-baki da kuri a kan sha’anin addini ba zai kai mutum ko ina ba
  • Wannan malami wanda yake koyar da ilmin larabci a jami’ar ABU Zaria ya ce zakulo baren karatu da yawan mabiya bai nuna baiwar ilmi

Zaria – Kabir Asgar ya ce idan aka duba lamarin a tsanake, za a ga cewa akwai abubuwan lura da yawa.

Ga wasu guda goma da ya tsinkaya da safen nan.

Kara karanta wannan

Ta bare: Saura kiris biki ango ya gano budurwarsa na da 'ya'ya 2, ya dauki tsattsauran mataki

1. Ƙara tabbatar da gaskiyar annabtar Manzon Allah (SAW). Dama haka al'amarin Shugaba (SAW) yake, duk sanda wani ya so ya taɓa darajar sa, to ba abin da mai ɓarnar zai cim ma wa sai taɓewa, shi ko Ma'aiki (SAW) ya ƙara samun daraja.

2. Cika baki da kuri akan harkar ilimi ba ya haifar da ɗa mai ido, ko da kuwa mutum na kan gaskiya ta fuskar ilimin da akida, ballantana kuma wanda ke kan subuha ko ɓata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

3. Gabatar da hankali ko tunani wasu bara-gurbi akan nassoshin Shari'a da fassarar magabata na ƙwarai hanya ce da kai mutum ga halaka.

4. Ba shakka game da cewa al'ummar ƙasar Kano da sauran Musulmin ƙasashen arewacin Nijeriya suna matukar ƙaunar Manzon Allah (SAW), saboda haka, mutum ya kiyayi yi wani shaidar cewa ba ya ƙaunar Manzon Allah (SAW) ba tare da hujja ƙwakkwara ba.

Kara karanta wannan

Jami'an Rundunar Tsaron Farin Kaya DSS, Sunyi Gaba Da Babban Dalibin Abdul-Jabbar Sabida Sabawa Dokar Zaman Kotu

5. Mu ci gaba da addu'ar neman dacewa da shiriyar Allah tare da gode masa akan ni'imar bin gaskiya. In ka ga Allah ya shiryasshe ka ka san ba dabarar ka ba ce, ni'imar sa ce, saboda haka ya zama wajibi ka gode masa.

Kabir Asgar
Dr. Kabir Asgar a Birnin Madina Hoto: @kabir.asgar.9
Asali: Facebook

6. Daga cikin abin da tarihi yake maimaituwa akai shine samuwar wasu waɗanda ake wa kallon masu hankali ko ilimi ko ƙaunar Ma'aiki (SAW) su gaza fahimtar ɓatan dake cikin maganganun Abduljabbar ko su yi tarayya da shi a kai ko su ƙudurce cewa an zalunce shi.

7. Gyaran ɓarna yana da sauƙi in gwamnati ta sa baki; An fi shekaru 20 ana jin wannan kasassaɓa daga bakin mai ita, malamai na ƙoƙarin su na warware shubuhohin sa ba tare da ya daina ba. Amma gwamnati ta yi maganin ɓarnar a shekara ɗaya da rabi.

8. Tara littafai da kutsawa cikin su ba tare da cikakken irshadin malaman ƙwarai ba ba ya mai da mutum malami. Hasali ma yana iya kai mutum ga halaka. Saboda haka, duk mai son samun ilimi mai nagarta to ya lazimci zama gaban malamai na ƙwarai.

Kara karanta wannan

"Ko ka zabi APC ko kaci Ubanka": Doguwa Yace kalamansa ba nufin zagi yake ba

9. Tarin mabiya da zaƙin baki da ƙarfin hali da zaƙule-zaƙulen maganganun da ba a saba ji ba, ba sa nuna ilimi ko ingancin fahimta. Ilimi mai nagarta shine bin koyarwar Alƙur'ani da Sunnah da bin fassarar magabata na ƙwarai.

10. Tasirin haɗin kan musulmi akan gaskiya ba ya ɓuya ga duk mai hankali. Saboda haka akwai tsananin buƙatar musulmi mu yi ƙoƙari mu bi gaskiya don kan mu ya haɗu ko ma samu mu yi maganin matsalolin da suka yi mana ɗaurin tankila.

Allah Ubangiji ya sa mu gama lafiya

Alkali Ibrahim Sarki Yola ya yi adalci

A wata sanarwa daga bakin Dr. Sa’idu Dukawa, an ji labari majalisar malaman Kano ta yaba da hukuncin da aka yi wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

Majalisar malaman addinin Musulunci na jihar Kano sun yaba da hukuncin Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, suka ce ya yi adalci wajen sauraron karar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng