Dakarun Sojin Sun yi wa ‘Yan Ta’addan Kwantan Bauna, Sun Halaka 4 a Borno
- Dakarun sojin kasan Najeriya kai harin kwantan bauna, sun yi nasarar sheke hudu daga cikin wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne a jihar Borno
- Kamar yadda Zagazola Makama suka ruwaito, hakan ya biyo bayan samamen da dakarun suka kai yankin kasuwar Daula cikin karamar hukumar Bama
- Dakarun sojin sun gano bindigu kirar AK47 da kekuna bakwai yayin samamen gami da budewa 'yan ta'adda wuta da suka yi a Borno
Borno - Dakarun sojin kasan Najeriya sun sheke 'yan boko Haram hudu yayin wani harin kwantan bauna da suka kai yankin kasuwar Daula cikin karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
Bama na daya daga cikin kananan hukumomin da 'yan bindiga ke cin kararensu ba babbaka a jihar Borno.
Kamar yadda Zagazola Makama, jaridar dake maida hankali a labarin yankin Cadi ta bayyana, wata majiyar sirri ta sanar da yadda harin kwantan baunan ya kasance a safiyar Juma'a.
"An gano yadda dakarun suka shirya samame ga 'yan ta'addan kafin fara musayar wuta dasu. Sunyi nasarar sheke hudu daga cikinsu yayin fafatawan.”
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
- Kamar yadda aka yanko maganar da majiyar ta fadi.
Dakarun sun gano bindigu kirar AK47 da kekuna bakwai yayin harin kwantan baunan.
Labarin yazo ne bayan makonni da dakarun suka kona wata mota dauke da mayakan ISWAP, inda ta sheke da yawan 'yan ta'adda da dama a musayar wutar.
Haka zalika, rundunar sojin a cikin watannin nan sun kai samame ga kungiyoyin 'yan ta'adda a Borno da saura dake fadin kasar.
ISWAP da Boko Haram Sun yi Arangama
A wani labari na daban, ‘yan ta’addan ISWAP da na Boko Haram dake jihar Borno sun yi gagarumar arangama inda aka halaka mayaka masu tarin yawa.
Bayan halaka wani kwamandan Boko Haram wanda shi ne Munzir a cikinsu, an gano cewa sun kwashi mayakansu don daukar fansa.
A maimakon su far wa mayakan ISWAP din da suka yi musu aika-aika, sun zagaya tare da zuwa wurin iyalansu.
A tare suka halaka mata 33 na mayakan ISWAP din inda suka kaddamar musu da kisan gilla a yankin tsaunikan Mandara dake jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.
Asali: Legit.ng