Fusatattun Mayakan Boko Haram Sun Yi Matan ‘Yan ISWAP 33 Kisan Gilla a Borno

Fusatattun Mayakan Boko Haram Sun Yi Matan ‘Yan ISWAP 33 Kisan Gilla a Borno

  • A wani harin daukar fansa da Boko Haram suka kaddamar kan mayakan ISWAP, sun zagaya har sansaninsu inda suka halaka matansu 33
  • A farko ‘yan Boko Haram sun samu jagoranci wani kwamanda Ali Ngulde wanda suka farmaki ISWAP a harin kwantan bauna a Yuwe, kuma suka yi nasara
  • Wata sabuwar arangamar tayi ajalin wasu mayakan Boko Haram da suka hada da kwamanda Malam Aboubakar da wasu mayaka 15 wanda ‘yan ISWAP ne suka yi

Borno - Fusatattun mayakan Boko Haram sun halaka a kalla matan mayakan ISWAP 33 a dajin Sambisa domin daukar fansan kisan Malam Aboubakar (Munzir) da wasu mayaka 15 da aka halaka a wata muguwar artabu.

Mayakan Boko Haram da ISWAP
Fusatattun Mayakan Boko Haram Sun Yi Matan ‘Yan ISWAP 33 Kisan Gilla a Borno. Hoto daga @ZagazOlamakama
Asali: Twitter

Tushen rikicin

Tun ranar 3 ga watan Disamba, wani babban ‘dan Boko Haram dake kula da tsaunin Mandara, Ali Ngulde, ya jagoranci daruruwan mayaka dauke da makamai domin yakar ‘yan ta’addan ISWAP dake dajin Sambisa.

Farmakin ya fara ne bayan an yi kokarin yin sasanci tsakanin kungiyar Boko Haram da ta ISWAP kan cewa su shirya yin mubaya’a ga shugabannin IS/ISWAP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zagazola Makama, wallafar da ta mayar da hankali wurin yakar ta’addanci a wuraren tafkin Chadi, ta gano cewa a rashin sanin kungiyar ISWAP, Ngulde da mayakansa sun yi kwantan bauna inda a kalla 12 daga cikin ‘yan ta’addan suka rasa rayukansu yayin da wasu suka tsere da raunika a Yuwe.

Bayan wannan arangamar, ‘yan Boko Haram sun kwace motoci kirar Hilux guda hudu daga abokan hamayyarsu kuma suka kone su.

Mayaka daga sansanin Abu Iklima sun shirya yaki

Wata majiya tace jim kadan bayan wannan nasarar, Boko Haram ta sake shirya mayaka daga sansanin Abu Iklima dake Gaizuwa, Gabchari, Mantari da Mallam Masari domin su kai hari kan ‘yan ISWAP dake Ukuba, Arra da Sabil Huda da Farisu inda aka halaka mayaka 23.

Bayan sa’o’i kadan, wani babban kwamandan ISWAP mai suna Ba’ana Chingori ya ayyana yaki kuma ya jagoranci mayaka domin su kai farmakin daukar fansa kan ‘yan Boko Haram dake Farisu.

Malam Aboubakar Munzir ya sheka lahira

Wannan farmakin kuwa ya kazanta inda ‘yan ISWAP suka halaka ‘yan Boko Haram 15 har da kwamandansu Malam Aboubakar tare da kwace babura bakwai daga hannunsu.

Daga bisani kungiyar ISWAP ta ja da baya kuma ta samu wurin zama a sansanin Izzah. Bayan nan sun koma Garin Abba wanda ke da nisan kilomita biyu kuma suka tsaya jiran Boko Haram.

Amma a maimakon su je su samu ‘yan ISWAP su cigaba da yakin, Boko Haram sun tafi kai tsaye inda matan mayakan ISWAP suke kuma suka halaka 33 daga ciki.

A cikin kwanakin nan za a ga yadda mayakan ISWAP zasu dauka fansa kan kisan gilla da Boko Haram suka yi wa matansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel