Wani Ango Ya Fasa Auren Budurwarsa Bayan Ya Gano Tana Da ’Ya’ya 2 Amma Bata Fada Masa Ba
- Babu abin da ya fi cin rai kamar gano gaskiya daidai lokacin da za a daura aure, gaskiyar ta zama mai ciwo
- Wannan wani sabon ango ne da ya shiga firgici yayin da ya gano wata gaskiya; budurwar da zai aure tana da ‘ya’ya biyu
- Ba tare da wani dogon tunani ba, ya yanke shawarin fasa auren sa’o’i kadan kafin a daura, jama'a sun yi martani
A wani mutum ya shiga tashin hankali yayin da ya gano gaskiya, ya fasa aurensa da budurwarsa bayan gano tana da ‘ya’ya biyu kuma bata taba fada masa ba.
Bala Baba Dihis ne ya yada yadda lamarin ya faru a Facebook, inda yace hakan ya faru da wani makusancinsa.
A cewar Bala, an shirya daura auren a ranar Asabar 17 ga watan Disamban wannan shekarar, amma aka samu wannan akasin.
An gano cewa, ta boye wannan lamarin ne ga wanda zai aureta, to amma gaskiya bata buya, kawai ya gano tarihinta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jama’ar soshiyal midiya sun shiga mamaki, sun kuma yi martani kan wannan lamari. Da yawa sun ga laifinta kasancewar ta yi kuskuren gina soyayya kan karya.
Martanin jama’ar Facebook
Ga dai kadan daga abin da mutane ke cewa:
AllaKaduna Nzeogwu:
"Ka ce wani abu.
“Mutumin kirki kamar ka bai kamata ya duba siyasa da addini ba kadai a matsayin hanyar neman adalci da kyautata a duniya.
“Sharri na zuwa ta hanyoyi da yawa. Ka yi magana ka kuma tallafawa wannan mtumin ya cika burinsa...an gina shi ne kan karya da yaudara. Za ka iya ceto mutane.”
Sonia Dash:
“Wasu dai kwakwalwar kansu an yi ta ne daga vibranium.
“Ba zan taba fahimtar dalilin boye ‘ya’ya ga wanda kake so ka aura ba. Kuma hakan na ci gaba da faruwa kullum.”
Arc Ehis Vheektor Onus:
“Akwai shawarwari da dama da za a iya yankewa a irin wannan lamarin...daya daga ciki kuma mafi gaggawa da zai kare faruwar rikici a gaba shine abin da mutumin ya yi...Shin hakan na nufin ahalin amaryar gaba dayansu babu mai hankali da zai shawarce ta ta yi abin da ya dace?”
Daniel Ogolo:
“Matar dai so take ta yaudare shi. Abin da ya yi ya burge ni. Ba batu ne na tana da ‘ya’ya ba (duk da cewa ya barka) batu ne na dakewar zuciyarta da kin fada masa babban lamarin rayuwa irin wannan. Irin wannan za ta iya ba mutum guba ta nuna ba ita ta yi ba.
Ba wannan ne karon farko da wani zai fasa aure bayan gano gaskiya ba. An sha yin hakan saboda tunanin rashin aminci a gaba.
Asali: Legit.ng