Gwamnatin Kano Ta Magantu Tace Zata Sanya Hannu Kan Hukuncin Da Aka Yankewa Abdul-Jabbar

Gwamnatin Kano Ta Magantu Tace Zata Sanya Hannu Kan Hukuncin Da Aka Yankewa Abdul-Jabbar

  • Tun lokacin da aka sami wani malamin makarantar firamare da kashe dalibarsa, dan ya karbi kudin fansa, gwamna ganduje yace zai sa hannu kan hukuncin kisansa.
  • Ya kan Zama ban-barakwai, ko sabon batu ace yau gwamna ya sanya hannu kan dokar kashe mutum wanda kotu tayi.
  • A tsawon shekara bakwai da gwamna Ganduje yayi a matsayin gwmanan jihar Kano bai sanya hannu kan hukuncin kisa ko guda daya ba

Kano: Kwamishinan Shari'a yace gwamna Abdullahi Umar Ganduje yace zai sa hannu kan hukuncin rataya da kotu ta yankewa Mallam Abduljabbar. kamar yadda Aminiya ta rawaito

Yace:

"Matsayar gwamna bai sauya ba kan sanya hannu akan hukunci da kotu ta yanke"
"Akwai matakan da ya kamata a bi kuma a shirye mai girma gwamna yake da zarar an kawo masa zai sanya hannu"

Kara karanta wannan

Daliban Abdul-Jabbar Sun Magantu Kan Hukuncin Da Kotu Ta Yanke, Sunce Akwai Lam'a

Kwamishinan ya ci gaba da cewa:

"Babu wanda za a bari ya taka doka, kuma an dauki duk matakin da ya kamata a dauka"

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mun gurfanar da Abduljabbar a gaban kotu ne domin bashi duk dama ta kare kansa, kuma Alhamdulillah kotu ta gamsu da hujjojin da muka gabatar shi yasa ta yanke masa hukunci"

A cewarsa hukuncin kotun ya wanke gwamnatin jihar Kano da ke nuna ba wani shafaffe da mai, sannan gwamnatin zata tabbatar da hakan bai sake faruwa ba

Ganduje
Gwamnatin Kano Ta Magantu Tace Zata Sanya Hannu Kan Hukuncin Da Aka Yankewa Abdul-Jabbar Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Ganduje Ya Ce Zai Sanya Hannu Kan Hukuncin Kisa Ga Wanda ya Kashe Hanifa

An sami wani malamin makarantar wata daliba mai suna Hanifa da laifin dauke yarinyar tare da boyeta da zummar karbar kudin fansa a wajen mahaifanta.

Sai dai kuma daga bisani malamin ya kashe dalibar tare da binne ta a makarantar da yake koyarwa.

Kara karanta wannan

Jami'an Rundunar Tsaron Farin Kaya DSS, Sunyi Gaba Da Babban Dalibin Abdul-Jabbar Sabida Sabawa Dokar Zaman Kotu

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta jagoranci wani atisaye da ya gano inda aka binne yarinyar tare da tonota.

An Gurfanar Dashi A Gaban Kotu

Bayan gurfanar dashi a gaban kotu wanda ake zargin ya musanta zargin da ake masa, amma da ga bisani kuma ya amsa.

Alkalin da ya jagoranci shari'ar ya yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga malamin su hanifa mai suna Abdul-Malik Tanko dan shima ya girbi abinda ya shuka.

Tuni dai gwamna Ganduje yace yana jiran fayil din yazo gabansa dan ya sanya hannu dan zartar masa da hukuncin.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida