Fada Ta Kaure Tsakanin Magoya Bayan Maroko da Faransa, Wani Yaro Ya Mutu
- An samu sabani tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafan Faransa da Moroko bayan wasan da aka buga jiya a kasar Qatar, wani yaro ya mutu a Montpellier
- Rikicin dai ya barke ne a yankuna daban-daban na kasar Faransa, ciki har da birnin Paris bayan da Faransa ta ci Moroko kwallaye 2 a wasan kusa da karshe
- Moroko ce kasar Afrika ta farko da ta taba nasarar hayewa zuwa wasan kusa da karshe a wasannin cin kofin duniya
Wani yaro ya mutu yayin da rikici ya barke tsakanin magoyo bayan Faransa da Moroko bayan kammala wasan kusa da karshe da aka gudanar a ranar Laraba 14 ga watan Disamba.
Rikicin ya barke ne a yankunan Faransa bayan da kasar ta lallasa Moroko da ci 2 da holoko a wasan da aka gudanar a filin wasan Lusail na kasar Qatar.
A cewar wani rahoton Sky Sports, wata sanarwa da ta fito daga ofishin karamar hukuma a Montpellier ta ce, an buge yaron ne da mota a lokacin da rikicin ya barke a birnin na Kudancin Faransa.
Daga baya an sanar da mutuwar yaron mai shekaru 14 a hukunace bayan kwantar dashi da aka yi a asibitin Montpellier, a cewar hukumomi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kafar yada labarai ta Faransa ta ce, an buge yaron ne da mota yayin da wani ya yi kokari sace tutar Faransa a jikin motar, lamarin da yasa ta kaucewa hanya.
‘Yan sandan Belgium sun kama magoya bayan kwallon kafa 100 bayan lallasa Moroko
A wani bangare kuma, akalla mutane 100 aka kama a birnin Brussels na kasar Belgium bayan da Faransa ta kori Moroko a wasan cin kofin duniya, DW ta ruwaito.
‘Yan sandan Belgium sun tabbatar da hakan, inda suka ce sun tsare mutanen ne bisa zargin tada hankalin jama’a, lalata motocin ‘yan sanda ta tayar da tarzoma bayan wasan na Faransa da Moroko.
Hakazalika, an kama mutane da yawa a Antwerp, biyo bayan barkewar rikicin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafan biyu a kasashen Belgium da Holland.
Haramta shan baraza ya taimakawa matan da suka zo kallon kwallo a Qatar
A wani labarin kuma, ba a sam rikici ko tashin-tashina a kasar Qatar tun bayan fara wannan wasa cin kofin duniya.
Majiyoyi da dama sun bayyana cewa, mata da suka halarci wasan sun ce, hana ayyukan alfasha a kasar ya ba su kwanciyar hankalin kallo.
A cewarsu, sam babu batun da ya shafi hantarar mata ko keta musu haddi kamar yadda aka saba gani a kasashen waje na turai.
Asali: Legit.ng