Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ya Yi Hadari, Ya Murkushe Wata Mata a Cikin Motarta a Abuja
- Jirgin kasan Abuja-Kaduna ya murkushe wata mata da ta hau kan layin dogo yayin da jirgi ke tafe
- Rahoton majiya ya bayyana cewa, matar mai matsakaicin shekaru ta tuko motarta ne kan titin da ke kusa da Kubwa
- A baya an yada hotunan yadda mutane ke aikin ceto yayin da jirgin ya wuce, ya yi kaca-kaca da motar
Kubwa, Abuja - Jirgin Abuja-Kaduna da ya dawo aiki kwanan nan ya murkushe wata mata mai matsakaicin shekara a kan titinsa a yankin Kubwa a babban birnin tarayya Abuja.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safiyar ranar Alhamis 15 Disamba, 2022, kamar yadda rahoton Channels Tv.
Wani shaidan gani da ido ya shaida cewa, lamarin ya faru ne mintuna kasa da biyar kafin jirgin ya isa tashar jirgin kasa ta Kubwa.
“Na Rasa Sukuni”: Dan Najeriya Ya Koka a Bidiyo, Ya ce Matar Da Ya Aura Ya Kai Turai Tana Sharholiya Da Maza
Ya shaida cewa, matar ta turo motarta kan titin jirgin ne domin wucewa, bata san jirgin yana tafe a guje daga jihar Kaduna ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam’ian tsaro sun tattara gawar matar zuwa asibti, an kuma dauke motar a layin dogon don kaucewa faruwar irin wannan hadarin a gaba.
Bidiyo ya nuna yadda jirgin ya murkushe mota, da wata mata a ciki
A wani bidyon da muka samo, an ga lokacin da motar ta makale a kan layin dogon yayin da jirgin ya murkushe ta.
Olisa Ogbechie Ik, wani ma'abocin Twitter ya yada wnai bidiyo da hotunan yadda lamarin ya faru, inda yace 'yan sanda sun shiga lamarin domin ceto jama'a.
Jirgin dai ya dawo aiki ne bayan shafe watanni kusan tara yana ajiye bayan da aka kai farmaki a kansa.
Wannan ne karon farko da aka bayyana samun matsala da jirgin kasan na Abuja-Kaduna tun bayan da gwamnati ta bayyana ci gaba da aikinsa a farkon wannan Disamba.
Jirgin Abuja-Kaduna ya dawo aiki a watan Disamba
A wani labarin kuma, kunji cewa, a farkon Disamba ne gwamnatin Najeriya ta amince a ci gaba da hawa jirgin Abuja-Kaduna.
An dakatar da jirgin ne bayan da 'yan bindiga suka kai hari kan fasojojinsa suka sace da yawa, suka hallaka wasu.
Ba sabon abu bane samun hadurra a Najeriya, musamman a kan titunan jirgin kasa ko na motoci.
Asali: Legit.ng