Martanin Jama’a Bayan Yankewa Sheikh Abduljabbar Hukuncin Kisa, Kwace Littafansa
- Kotu ta yankewa Sheikh Abduljabbar Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan shafe watanni ana sauraran hujjoji
- Jim kadan bayan yanke hukuncin ne jama'a a bakin kotu suka shaidawa Legit.ng Hausa abin da suka ji da wannan hukunci
- Jama'ar kafar sada zumunta sun bayyana kadan daga ra'ayoyinsu kan wannan babban hukunci mai daukar hankali
Jihar Kano - A yau ne aka yankewa malamin addinin Islama, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kama shi da laifin batanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu SAW.
Wannan lamari dai ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta, domin kuwa an jima ana sauraran me zai faru, gashi karshen lamari ya zo.
A rahoton da muka tattaro, jama'a da dama sun yi martani tare da bayyana matsayarsu kan wannan hukunci da aka yankewa malamin.
Wakiliyar Legit.ng Hausa a jihar Kano ta halarci zaman kotun, ga kadan daga martanin jama'a da ta tattaro mana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Martanin jama'a bayan hukuncin kotu
Musa Bello wani magidanci da ke zaune a kofar kudi yace:
"To mu dai bamu da abinda zamu ce dai Allah ya kare wani da aikata irin wannan danyen aikin da sunan kare ma'aiki."
Isma'il yace
"Alhamdulillah, Alhamdulillah, mun yiwa Allah godiya bisa wannan hukuncin"
Wani dalibinsa da bai bayyana sunan sa ba cewa ya yi:
"Yana da damar da zai iya daukaka kara, kamar yadda kotu tace, ni dai abinda nake gani shine ba'a fahimceshi ba- inji wani dalibinsa da bai bayyana sunan sa ba."
Wani dan Jarida mai zaman kansa, Abubakar Muhd:
"Abin jira a gani shine mu ga abinda gwamnati zata ce kan wannan batun"
Martanin 'yan Twitter
A fannin kafafen sada zumunta, ga kadan daga abin da mutane ke cewa:
@ishaq_Marafa01 yace:
"Alhamdulilah mashallah. Wannan alkali yayi abinda ya dace. Allah ubangiji ya kara mana son Fiyayyen Halitta S.A.W. Amin."
@Yousuuffff yace:
"Alhamdulillah! Abduljabar ka karbi wnn hukunchi kawai kahutawa kanka."
@KhadijaKabirAb4 tace:
"Gsky sarki Yola Allah Maka albarka wanin hukunci yayi daidai yy mun dadi Allah ya qara tarwatsa duk wani Wanda zai kwantanta irin haka Allah Kuma qara nauyii qasa Lahira na cin na jira Annabi SAW ba Abu wasa banii Allah ya nuna Maka Iko sa sai ma kaji lahira zaka gani Inshallah."
Alamu dai sun nuna jama'a a kasar nan sun fi mai da hankali tare da amincewa da hukuncin da aka yanke ma wannan malamin.
Asali: Legit.ng
Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.
AbdulRahman Rashida