An Maka Gwamna El-Rufai da Masarauta a Kotu, Ana Neman a Tunbuke Sarkin Zazzau

An Maka Gwamna El-Rufai da Masarauta a Kotu, Ana Neman a Tunbuke Sarkin Zazzau

  • Tsohon Wazirin Zazzau, Ibrahim Muhammad Aminu yana kalubalantar nadin Ahmed Nuhu Bamalli
  • Rabiu Saidu shi ne Lauyan da ya tsayawa tsohon ‘dan majalisar nadin Sarkin a shari’arsa da masarauta
  • Ibrahim Muhammad Aminu ya ce Gwamnatin Nasir El-Rufai ta saba doka wajen nada sabon Sarki a 2020

Kaduna - Tsohon ‘dan majalisar nada Sarkin Zazzau, Alhaji Ibrahim Muhammad Aminu ya shigar da kara a kotu a kan nadin Amb. Ahmed Nuhu Bamalli.

Daily Trust ta rahoto cewa Ibrahim Muhammad Aminu wanda ya rike Wazirin Zazzau yana kalubalantar Gwamna Nasir El-Rufai da wasu mutane 12.

Sauran wadanda ake kara sun hada da Mai martaba Sarkin Zazzau da kuma tsohon Limamin Kona, Marigayi Malam Sani Aliyu wanda ya rasu shekarar bara.

Alhaji Ibrahim Muhammad Aminu ya roki babban kotun jiha da ke Kaduna ta soke zaben Ahmed Nuhu Bamalli da aka yi a matsayin Sarkin Zazzau na 19.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Tinubu, Ganduje, El-Rufai na can a Kaduna don kaddamar da kamfen APC a Arewa maso Yama

Me ya kai magana kotu?

A ranar Laraba aka dauko wannan kara, amma Alkali Isah Aliyu ya dage shari’ar sai zuwa ranar 23 ga watan Fubrairu domin a fahimci karar da ake yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lauyan da ya shigar da kara, Rabiu Saidu, ya shaidawa manema labarai cewa suna zargin ba a bi doka wajen nada Ahmad Bamalli a matsayin Sarki ba.

Sarkin Zazzau
Mai martaba Ahmad Bamalli da Gwamna Nasir El-Rufai Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

“A al’ada, ‘yan majalisar nadin Sarki suke aikawa Gwamnan jiha sunaye, kuma ana zaben sunayen nan ne daga na farko zuwa na karshe.
Saboda haka daga cikin korafinmu, muna cewa wanda yake kan kujerar Sarki bai cikin sunayen da ‘yan majalisa suka aikawa Gwamna.
Kuma bai cikin wadanda suka cancanta a aika da sunansu, saboda haka nada shi Sarki ya sabawa shawarar da aka ba Mai girma Gwamna.”

- Rabiu Saidu

Jaridar Sun ta ce Lauyan ya bukaci Alkali ya tunbuke Mai martaba Ahmad Nuhu Bamalli daga sarauta, ya nada Alhaji Munir Jafar ko wani daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Gwamna El-Rufai Ya Jero Abubuwa 2 da Za Su Hana Shi Zama Sanata Bayan Barin Mulki

Lauyan da yake kare masarautar Zazzau, Aminu Usman Bamali ya ce ya kamata Saidu ya bada adireshinsa na garin Kaduna domin a Abuja yake zama.

Nasabar Bola Tinubu

An ji labari Bode George yana jayayya da asalin tsohon Gwamnan jiharsa, ya ce sam babu hujjar da ke nuna ‘Dan takaran APC, Bola Tinubu daga Legas ya fito.

Bayan haka, an ji Cif Bode George ya nuna muddin ba a shawo kan rikicin gidan jam’iyyar PDP ba, ba zai zabi Atiku Abubakar da aka tsaida masu takara ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng