Kotun Kano ta yankewa tsohon da hisbah hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kotun Kano ta yankewa tsohon da hisbah hukuncin kisa ta hanyar rataya

  • Wani tsohon jami’in Hisbah ya shiga tasku yayin da kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya
  • An kama Dayyabu Muhammad ne da laifin kashe wata bazawararsa da ya nema saboda an hana shi aurenta
  • Hujjoji sun kankama a gaban kotu, bayan shekaru sama da 10 an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya

Jihar Kano - Dayyabu Muhammad, wani tsohon dakaren Hisbah ya gamu da fushin alkali yayin da aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya a wata kotun jihar Kano mai lamba 9.

Mai shari’a Amina Adamu ce ta yanke hukuncin bayan da ta kama jami’in na Hisbah da laifin kashe bazawarsa mai suna Hauwa.

Laifin kisan bazawarar tasa ya saba doka, don haka aka yanke masa hukunci daidai da kunfin Panel Code sashe na 221.

Kara karanta wannan

Tinubu ga 'yan Kaduna: Ni na san yadda zan kawo karshe 'yan bindiga, ku zabe ni na gaji Buhari

An yanke ma dan Hisbah hukuncin kisa a Kano
Kotun Kano ta yankewa tsohon da hisbah hukuncin kisa ta hanyar rataya | Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Alakar Dayyabu da Hauwa da hukumar Hisbah

Rahoton da muka samo daga Aminiya ya bayyana cewa, Dayyabu ya kasance almajiri a gidansu Hauwa, kuma jami’i ne na Hisbah wanda ya nuna sha’awarsa ta auren Hauwa, daga nan suka kulla soyayya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da Dayyabu ya zo da maganar aure, iyayen Hauwa sun ce ba za su bashi ita ba saboda suna ganin akwai tangarda a tarbiyyarsa, wannan yasa Hauwa daga baya ta sauya ra’ayi a kansa, tace bata yi.

Yadda Dayyabu ya kashe Hauwa

Wannan lamari dai ya fusata Dayyabu, inda ya zo har gida a shekarar 2011 har daki ya nemi ganin Hauwa.

An ruwaito cewa, a nan ya dauko wuka ya caccaka mata a jikinta, kuma wannan dai shi ne sanadin mutuwarta.

Bayan samun gamsassun hujjoji, mai shair’a Amina Adamu ta ce ta gamsu da komai da aka gabatar na hujja, don haka ta yanke masa hukunci.

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Jigo a Najeriya ya fusata kan kin hukunta wadanda suka kashe Deborah

Yanzu dai an yanke masa hukunci ta hanyar rataya, amma ba a san ko hakan zai tabbata ba, domin ana yanke hukunci a samu sabanin hakan.

An yankewa malamin makaranta kisa ta hanyar rataya

Wannan dai na zuwa ne watanni kadan bayan da aka yankewa wani malamin makarantan da ya kashe dalibarsa bayan da ya sace ta.

An kama Abdulmalik ne tare da gurfanar dashi a gaban kotu bisa laifin kashe dalibarsa mai shekaru kanana da gubar bera.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.