Fitaccen limami: Yadda Na Kubuta Daga Harin 'Yan Boko Haram a Masallaci a Kano

Fitaccen limami: Yadda Na Kubuta Daga Harin 'Yan Boko Haram a Masallaci a Kano

  • Babban limamin jihar Kano, Farfesa Sani Zahradeen ya magantu a kan harin da Mayakan Boko Haram suka kai masallacin jihar Shekaru bakwai da suka wuce
  • Farfesa Zahradeen ya ce ya gama huduba kenan zai tada ikama sai ya ji karar fashewar abu daga nan sai tashin karar harbe-harbe
  • Ya ce a lokacin da abun ya faru, an shafe kimanin awa daya ana abu guda yayin da su kuma suke cikin masallacin

Kano - Farfesa Sani Zahradeen, babban limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a lokacin da Boko Haram suka kai hari babban masallacin Juma'a na Kano a 2014, ya bayyana yadda ya tsallake rijiya da baya.

Mayakan kungiyar ta'addancin sun kaddamar da kazamin hari a babban masallacin Juma'a suka dana bama-bamai da harbin masallata har lahira a ranar 28 ga watan Nuwamban 2014, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zulum ya Kaddamar da Yakin Neman Zabensa na 2023 a Borno

Farfesa Sani Zahradeen
Fitaccen limami: Yadda Na Kubuta Daga Harin 'Yan Boko Haram a Masallaci a Kano Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Fiye da mutum 200 ne suka mutu a harin wanda ake ganin an shirya kaddamar da shi ne a kan tsigaggen sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Yadda lamarin ya faru shekaru bakwai da suka wuce

Farfesa Zahradeen, wanda shine babban limamin masarautar Kano, ya ce harin ya shafe kimanin awa daya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake bayanin lamarin a wata hira da Trust TV, limamin wanda shine shugaban jami'ar Bayero (BUK), ya ce:

"Kimanin shekaru bakwai kenan wanda ya faru a ranar 28 ga watan Nuwamban 2014, na gama karanta Khudba sannan muna shirin tayar da sallah, lokacin da nace Allahu Akbar sai na ji Boom a bayana amma ban gane akwai wani abu ba.
"Amma daga bisani kafin na fara karanta Al-Qur'ani, sai mutane suka fara ihun Allahu Akbar, Allahu Akbar a bayana, 'dana na kokarin ganin abun da ke faruwa, wasu mutane na kuka sannan akwai karar harbe-harbe a waje.

Kara karanta wannan

Yadda Wani Gwamnan Najeriya Ya Baje Kolin Girki, Ya Rangada Miyar Farfesun Kifi

"'Dana da ya kai ni masallaci ya shigo yana kokarin fita waje sai nace a'a a'a suna harbi a waje, mun tsaya cikin masallaci na kimanin awa daya."

Sarki Sanusi II na Umra lokacin da abun ya faru

Da aka tambaye shi inda sarkin yake a wannan lokacin, limamin ya ce:

"Sarkin baya masallaci a wannan lokacin, baya kasar, yana umra amma ya ji labari, ya kira ni sannan yace yanzu na ji labarin abun da ya faru, muna kammalawa, Insha Allah ina hanya gobe."

Kan adadin mutanen da suka mutu, limamin ya ce:

"Hukuma sun ce mutum fiye da 100 ne suka mutu amma wani ya fada mun cewa mutum fiye da 500 ne auka mutu, don haka yau shekaru bakwai kenan kuma Insha Allah za mu yiwa mamatan addu'a."

Tinubu ya yi alkawarin murkushe yan ta'adda a arewa idan ya gaje Buhari

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na APC a zaben 2023, Bola Tinubu ya ce idan har ya yi nasarar darewa kujerar Shugaba Buhari toh lallai gwamnatinsa za ta murkushe yan ta'adda a yankin arewa.

Kara karanta wannan

Iyalai A Nigeria Na Hakura Da Ci Su Koshi Sabida Yanayin Tashin abinci

Tinubu ya dau alkawarin ne a Birnin Gwari da ke jihar Kaduna a yayin da ya kai ziyarar jaje masarautar yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng