Kasar Jamus Ta Kirkiro Injin Kyankyashe Jajirai Cikin Sauki
- Kasar Jamus ta zo da wani sabon salon samun jarirai ba ta hanyar haihuwa ba, ta hanyar amfani da inji
- An kirkiri injin kyankyasan jarirai, wanda zai ba da damar haihuwa ba tare da wata matsalar wahalar ciki ba
- Wani bidiyo ya bayyana dalla-dalla yadda aka tsara injin da kuma ayyukan da zai yi da ma yadda iyaye za su mu'amalanci jariransu
Berlin, Kasar Jamus - A wata fasaha mai daukar hankali kuma da ka iya sauya yadda ake ganin duniya, kasar Jamus ta kirkiri injin kyankyasar jarirai.
Rahotanni daga duniyar fasaha sun bayyana cewa, wannan ne karon farko da aka samu irin wannan fasahrar kyankyasa mai sarrafa kanta a diniya.
Injin kyankyasan da aka lakaba masa suna ‘Ecto Life’ an ce zai hutar da iyaye da ke da sha’awar haihuwa amma suke da wata nakasa ta mahaifa ko dai radin kansu na gudun wahalar haihuwa.
An ruwaito cewa, shekaru sama da 50 aka shafe ana yin wannan aiki, kuma masana da manyan liktoci ne suka dukufa wajen tabbatar da faruwar lamarin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A bangaren samar da jarirai, an ce injin zai iya samar da akalla jarirai 30,000 duk shekara.
Wani bidiyon gwaji da Hashem Al-Ghaili ya yada a kafar Facebook ya nuna dalla-dalla yadda injin ke aiki da kuma matsalolin da zai warware ga mata masu matsalar haihuwa da mahaifa.
Batun rasa rai a wurin haihuwa, an yi imanin cewa, wannan injin zai rage adadi mai yawa idan ya tabbata za a yi amfani dashi.
A duniya, akwai kasashe da dama da ke fuskantar raguwar adadin jama’a, irinsu Japan, Bulgeria da Koriya ta Kudu, bidiyon ya ambaci cewa, tabbas irin wannan inji ka iya zama mafita gare su, kakarsu ta yanke saka.
Yadda iyaye za su iya mu’amalantar jariransu suna gida
A bidiyon da wakilin Legit.ng Hausa ya gano, an ce injin yana hanyoyin da aka tsara shi ya ba iyaye damar magana, lakkana kalmomi, koya musu yare da dai sauransu.
Yadda hakan zai yiwu kuwa, akwai kamerori da yawa a cikin injin kyankyasan da aka lika a jikin wata manhajar da za ta ke kai dukkan bayanai da ke da muhimmanci ga iyayen jarirai.
A bangaren gani da ido, injin yana amfani da fasahar VR mai gani har hanji da ka iya ba iyaye damar gani tare da jin kamar suna taba jariransu.
Batun harbi da naushi da mai juna biyu ke ji, injin dai na da tanadin haka ta hanyar amfani da VR.
Iyaye za su iya sauke manhajar wayan hannu da za ta ba su damar sanin halin da jariri ke ciki a bidiyon kai tsaye da ke nuna yanayinsa.
Hakazalika, injin yana daidaita yanayi daidai da bukatar dumi ko sanyi na cikin mahaifar uwa kamatr yadda yake a al’adance.
Kalli bidiyon:
A jihar Kano kuwa, wani jariri mai shekaru kasa da biyu ya fada rijiya, rahoto ya bayyana yadda lamarin ya faru.
Asali: Legit.ng