Miji Ya Karya Azumi Tsabar Wahala, Matarsa Ta Kama Shi Yana Kwasar Tuwo da Tsakar Rana
- Wata mata ‘yar Najeriya ta kadu yayin da ta kama mijinta na kwasar abinci yayin da yake azumi tare da ita
- A cikin wani bidiyo mai ban dariya, an ga lokacin da mijin ya buya a kasan teburin cin abinci da katon farantin tuwo da miya
- Matar cikin mamaki ta dauki bidiyon mijin nata, wanda ya bayyana karara cewa ba zai iya kai azumin da ya dauka ba
Wata mata ‘yar Najeriya ta shiga mamaki yayin da ta gano mijinta ya karya azumin da ya dauka, ya buya yana kwasar tuwo a kasan teburi.
Matashin mutumin da aka gani a bidiyon tare da matarsa sun dauki azumi ne na kwanaki shida domin yiwa ahalin addu’o’in nasara.
Sai dai, matar kawai ka ga mijinta kwatsam a karkashin teburin cin abinci yana kwasar tuwo da miya, lamarin da ya sa ta fara daukarsa bidiyo.
An ga lokacin da mutumin ke gaban tulin tuwo da miya, ga kuma abin sha kamar dai wanda ba azumi yake ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yada bidiyon a TikTok tare da cewa:
“Ina zaton muna azumi ne. Kana nan kana cin abinci. Ba kamata ya yi ka yi azumi ba? Kamata ya yi mu yi azumin kwanaki 6 amma wannan ne na uku gashi ka fara cin abinci. Haka ya kamata mu yi azumin kenan. Ka zo ka dafa eba mai kyau har da nemo abin sha.”
Bayan kama shi hannu dumu-dumu, mutumin ya ce ya fasa azumin ne saboda yana tsoron mutuwa.
A cewarsa:
“A cikin gida na sai na buya kafin na ci abinci. Na yi kokari fa. So kike ki kashe ni? Ya isa haka.”
Kalli bidiyon:
Martanin jama’a a kafar TikTok
Bayan yada bidiyon, mutane da dama sun nuna sha’awarsu ga wannan bidiyon, ga dai abin da suke cewa:
@ruthyomi2021:
“Yana rike da injila mana, a ci gaba da azumi. Matukar yana rike da injila ai azumi bai karye ba.”
@miles_a33:
“Ina kaunar gaskiyar cewa ka gane addu’arka ta karbu. Ci gaba da cin abinci kawai.”
@patrickferris181:
“Dan uwa na ka gama. Matata ba ta bari na yi sakat.”
@sebastine_jr:
“Dan uwa na buya ya ci ko da kuwa itace ruhu mai tsarki.”
@rempsa2411:
“Shin kunga yadda hannunsa ke musayar injilar daga wannan teburin zuwa wani.”
@dwealthyk:
“Ya kai da na, tashi ka ci domin kuwa an amsa addu’arka. Eba abin ceto ne. Mac ka tuba.”
Daya daga abin da 'yan Najeriya ke more rayuwarsu dashi bayan cin abinci shine kayan kwalba, abubuwan sha masu zaki da ba sa bugarwa, rahoto ya fadi yadda ake shirin kakaba musu haraji.
Asali: Legit.ng