Sojin Sama Sun yi Lugude kan ‘Yan Bindiga Har Sansanoninsu Dake Dajikan Kaduna

Sojin Sama Sun yi Lugude kan ‘Yan Bindiga Har Sansanoninsu Dake Dajikan Kaduna

  • Dakarun sojin saman Najeriya sun yi nasarar sheke 'yan ta'adda da dama a Birnin Gwari, Igabi da karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna
  • Hakan yazo ne bayan samamen da rundunar ta kai a sansanin 'yan ta'addan ta hanyar amfani da harsasai masu linzami wajen tarwatsa sansaninsu
  • Dakarun basu tsaya a nan ba, sai da suka tarwatsa gidan gawurtaccen shugaban 'yan ta'adda, Alhaji Lawan, duk da ba a tabbatar ko ya rasa ransa ba

Kaduna - Dakarun sojin saman Najeriya sun yi nasarar sheke 'yan ta'adda da dama a Birnin Gwari, Igabi da karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.

Kwamishinan kula da lamurran tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana yadda aka sanar da hukumomin tsaron gwamnatin jihar bayanan ayyukan.

Jiragen yakin soji
Sojin Sama Sun yi Lugude kan ‘Yan Bindiga Har Sansanoninsu Dake Dajikan Kaduna. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

Aruwan ya bayyana yadda sojin saman Najeriya yayin cigaba da sintiri a fadin jihar Kaduna suka ruwaito yadda 'yan bindiga da dama suka rasa rayukansu, gami da tarwatsa sansaninsu a samamen da aka kai musu cikin kwanakin nan.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Daukarwa Al'ummar Kaduna Da Arewa Wani Babban Alkawari Idan Har Ya Gaje Buhari

Jami'an da suka kai samame cikin kwanakin nan sun gano gami da kai farmaki yankin Kasarami dake karamar hukumar Chikun.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An ragargaza gidan shugaban 'yan bindiga, Alhaji Lawan

A harin da dakurun suka kai, sun yi nasarar kai farmaki gami da tarwatsa gidan shugaban tawagar hatsabiban, Alhaji Lawan.

Ba a tabbatar ko an sheke shugaban 'yan ta'adda ba yayin samamen.

"Haka zalika, an yi nasarar tarwatsa sansanin 'yan bindiga da harsasai masu linzami, inda aka tarwatsa sansaninsu na dajin Kofita da Kuyanbana cikin karamar hukumar Birnin Gwari."

- Aruwan yace.

Har ila yau an hara gami da tarwatsa sansaninsu da dama a Kuduru da Gonan Baturiya, inda aka sheke 'yan ta'adda kimanin kilomita hudu a gabashin Nabango.

"Gwamnatin jihar Kaduna ta samu rahoto tare da godiya gami da jinjinawa jami'an tsaron bisa nasarar da suka yi yayin samamen. Za a cigaba da sanya ido tare da bada tsaro ga yankin,"

Kara karanta wannan

Zulum ya Kaddamar da Yakin Neman Zabensa na 2023 a Borno

- cewar Aruwan.

'Yan Sanda sun yi ruwan wuta kan 'yan bindiga, sun ceto mutum biyar

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da yin musayar wuta da 'yan bindiga inda suka damke biyu dagaa ciki.

An yi nasarar ceto mutum biyar da miyagun suka kwaso da zummar yin garkuwa dasu a karamar hukumar Kurfi ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng